Jami’ar da ake Karatu daga Gida, wadda aka fi sani da ‘National Open University of Nigeria’ (NOUN), za ta gudanar da bikin yaye dalibai har 20,799.
A tarihin yaye dalibai, wannan ne karo na farko da wata jami’a a fadin Afrika ta Yamma za ta yaye dalibai masu yawa kamar haka.
Da ya ke tattaunawa da manema labarai yau a hedikwatar NOUN da ke Abuja, Shugaban Jami’ar, Farfesa Abdalla Adamu, ya ce daga cikin wadanda za a yaye din akwai har guda 103 wadanda suka samu takardar shaidar kammala digiri mai daraja ta daya, wato First Class.
Wannan shi ne karo na takwas da NOUN za ta yaye dalibai, wanda za a gudanar a ranar Asabar, 23 Ga Maris, a harabar hedikwatar jami’ar, wadda ke kusa da sabuwar hedikwatar EFCC, a Gundumar Jabi, Abuja.
Adamu ya ci gaba da cewa NOUN ta kara samun gagarimin tagomashi a ranar 7 Ga Disamba, 2018, ranar da Shugaba Muhammadu Buhari ya sa hannu a kan Dokar da Aka Yi Wa Garambawul ta NOUN.
Ya ce wannan garambawul da aka yi wa gokar ya zai bai wa daliban NOUN dama ta tilas domin su rika tafiya aikin bautar kasa, wato NYSC, sannan kuma wadanda suka karanci fannin shari’a za su rika samun damar wucewa Makarantar Koyon Aikin Shari’a da Lauya ta Kasa.
Shugaban jami’ar ya ce daga lokacin da aka saw a dokar hannu, to NOUN ta zama daidai da kowace jami’a a kasar nan.
“A yanzu dai mu na kan mataki na Tattaunawa da hukumomin da ke kula da Makarantar Koyon Aikin Shari’a da kuma NYSC domin ganin an fito da ka’idojin da za mu rika bi mu na tura daliban mu.
“A shirye mu ke mu bi kowace irin ka’ida ko sharuddan da suka gindaya mana.
“Zan sake yin amfani da wannan daman a shaida muku cewa NOUN ta zama uwar jami’a wadda ita kadai ce ke goya masara gata da kuma wadanda suka yanke yakinin samu ilmi a rayuwar su ta duniya.
“NOUN ce kadai ke bayar da dama ga daurarrun da ke zaman bursuna a gidajen kurkuku domin su yi ilmi kyauta a lokacin da suke a tsare.
Daga nan sai ya fayyace cewa a yanzu akwai daurarru sama da 400 wadanda ke karatu a karkashin NOUN, amma su na a tsare a kurkuku.
Ya ce ba su biyan kudin rajista, kuma kyauta ake samar musu da kayan karatu, ciki kuwa har da kwamfutoci.
“Akwai ma wanda ke kwas na digirin digirgir, wato Phd a karkashin NOUN, duk kuwa da cewa an yanke masa hukuncin kisa, ya na tsare a kurkuku. Mu na kuma sa rai idan ya kammala za mu dauke shi aiki a NOUN.
Abdalla ya tunatar da cewa ko bayan da tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo ya kammala karatun sa na digirin digirgir a NOUN, an dauke shi aikin kula da wasu dalibai, a reshen NOUN da ke Abeokuta, inda aka bude masa ofis kuma aka hada shi da dalibai biyu domin ya rika kula da su.
“Alawus na naira 40,000 kacal mu ke biyan sa a duk shekara. Haka ake biyan duk wanda mu ka dauka a matsayin mai kula da daliba. Kuma shi ma Obasanjo ya na jin dadin dan alawus din da mu ke ba shi.”Inji Abdalla.