JAMB ta bayyana ranar rubuta jarabawar shiga jami’oi na 2019

0

Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Jami’o’in Kasar nan (JAMB) ta bayyana cewa za a rubuta jarabawar shiga jami’o’in kasar nan ranar 11 ga watan Afrilu.

Hukumar ta kuma canja ranar rubuta jarabawar gwaji wato Mock Examinations daga ranar 23 ga watan Maris zuwa 1 ga watan Afrilu.

Idan ba a manta ba hukumar JAMB ta fara siyar da fom din JAMB tun a ranar 10 ga watan Janairu sannan ta rufe siyar da fom din ranar 21 ga watan Fabrairu.

A lokacin ta tsayar da ranar rubuta ainihin jarabawar ranar 16 zuwa 23 ga watan Maris amma dage zabe da aka yi ya sa hukumar ta dakatar da rubuta jarabawar.

Share.

game da Author