Jagoran APC ya barke da kuka, jin sanarwar Gwamna Ortom ya lashe zaben Benuwai

0

Jagoran APC a jihar Benuwai, kuma tsohon Shugaban Kungiyar Dalibai ta Najeriya, NANS, Daniel Onjeh, ya barke da kuka jiya Lahadi, jin sanarwar Gwamna Samuel Ortom na Jihar Benuwai ne ya lashe zaben gwamna.

Onjeh, wanda ya barke da kuka a garin su, Ogbadibo, yace ya na kukan takaicin tunanin irin mawuyacin halin da al’ummar jihar Benuwai za su fada ne.

Ya ce bai san irin yadda ko al’ummar jihar za su sake hakuri da juriyar wasu shekaru hudu tsananin halin kunci a karkashin gwamnatin Ortom ta PDP ba.

Ya kuma kara da cewa bai tabbatar ko Shugaba Muhammadu Buhari zai sake sakar wa gwamnatin jihar Benuwai kudaden ceto jihohi daga fatara ba da kuma na Paris Club.

Dalili, Onjeh cewa ya yi Ortom bai yi bayani dalla-dallar yadda ya yi da kudaden da aka ba shi a baya ba, domin yi wa jama’a aiki.

Onjeh ya yi maganar rashin biyan albashi, alawus, fansho da garatuti na daga cikin matsalar da gwamna Ortom ya kasa warwarewa a tsawon shekaru hudu da ya yi ya na mulkin jihar Benuwai.

Share.

game da Author