Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta ce Zaben Gwamnan Jihar Adamawa bai kammalu ba.
Babban Jami’in INEC mai bayyana sakamakon zabe, Farfesa Andrew Haruna, ya ce hakan ya kasance bisa hujjar cewa bambancin kuri’un da ke tsakanin APC da PDP ba su kai yawan kuri’un da aka soke a kusan rumfuna 40 ba.
Ya ce an soke kuri’u 40,988 a rumfunan zabe 44 a fadin jihar.
Bambancin kuri’u 32,476 ne tsakanin ‘yan takarar biyu da ke da rinjaye fiye da sauran masu takara.
Andrewa ya karanto dokar INEC wadda ta ce idan irin haka ta faru, zabe bai kammalu ba kenan, ba za a fadi wanda ya yi nasara ba.
A lokacin da ya yi wannan bayani, dan takarar PDP Ahmadu Fintiri ne ke kan gaban Gwamna Bindow na APC da yawan kuri’u. Fintiri na da 367,471, Bindow kuma 334,995.
Na ukun su jam’iyyar ADC na da 113,205.
INEC ta ce za ta bayyana ranar zabe zagaye na biyu domin a fitar da wanda ya yi nasara.