INEC ta ce za ta karasa zabukan da za a sake a Jihar Bauchi

0

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa ta bayyana cewa za ta karasa zabukan da suka rage wadanda za ta maimaita a wasu yankunan Jihar Bauchi.

Kakakin Yada Labarai na INEC, Festus Okoye, ya ce hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta yi, inda ta dakatar da ci gaba da tattara sakamakon zaben Karamar Hukumar Tafawa Balewa, ta ce hukuncin bai shafi sauran yankunan da za a gudanar da zabuka ba.

Umarnin dai ya dakatar da ci gaba da tattara sakamakon zaben Tafawa Balewa ne, tare kuma da hana bayyana sakamakon zaben da aka bayyana.

Tun da farko dai matasa ‘yan jagaliya ne suka kekketa takardar da sakamakon zaben ke ciki.

Hakan ya sa Babban Jami’in Zabe na Jihar Bauchi ya ki amincewa da sakamakon a aka mika masa a kan takardar da ba ita ce ya kamata a rubuta sakamakon zaben ba.

Har zuwa lokacin da aka dakatar da bayyana sakamakon zaben dai Bala Mohammed ne na jam’iyyar PDP ke gaba a kan Gwamna Abubakar na Bauchi na jam’iyyar APC.

Share.

game da Author