Abubakar Umar tsohon makaho ne mai shekaru 50 da ya shigar da kara a kotun shari’a dake Magajin Gari a jihar Kaduna domin kotu ta kwato masa radiyon sa da kudin gyaran da ya biya Naira 350.
Umaru ya bayyana cewa ya dauki ‘yar radiyonsa ya kai wa Garba Abubakar dake da shago a Sabon Gidan Guragu a Kano road a Kaduna domin a gyara masa amma sai hakan bai yiwu ba.
‘‘Wannan radiyo itace kadai abin dake dauke mun kadaici da kewa a rayuwata sannan da kyar na samu na biya kudin gyaran radiyon amma Abubakar ya ki gyara min.
” Kulum idan na je shagon sai na ji yana yi wa mutanen shagon radan cewa a fada min cewa baya nan ya yi tafiya.
Umaru yace ya gaji da yawon zuwa shagon Abubakar yana rokon kotu ta karbo masa radiyon sa.
Abubakar ya bayyana wa kotun cewa ya gyara radiyon amma ya boye radiyon ne saboda dukan mutanen shagon da Umaru ya yi.
” Umar na da fushin tsiya haka kawai a wani rana ya zo ya doddoke mutanen dake shagona don an ce masa bana nan.
Alkalin kotun Musa Sa’ad-Goma ya sa Abubakar ya kawo radiyon kotu domin kotu ta tabbatar lallai an gyara.
Bayan haka kotu ta mika wa Umar radiyon domin ya tabbatar radiyonsa ne kuma tana aiki.
Da Umar ya taba radiyon sai ya ce radiyonsa ne amma wajen canza tasha da yanayin rediyon gaba daya ba daidai suke ba.
Alkali Sa’ad -Goma ya gargadi Umar da kada ya sake zuwa shagon Abubakar cewa za a sasanta su a kotu.