Ikirarin yawan kuri’un da Atiku ya ce ya samu, cike ya ke da bankaura da Lissafin-Dawakan-Rano

0

Lissafin yawan kuri’un da dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya ce ya samu a zaben shugaban kasa da aka gudanar a cikin watan Fabrairu, cike ya ke da harankazama da lissafin-dawakan-Rano.

Atiku Abubakar ya yi ikirarin cewa ya fi Shugaba Muhammadu Buhari samun yawan kuri’u a zaben. Sannan kuma ya ce ya samu hujjar sa ne daga runbun na’urar da INEC ke killace alkalumman sakamakon zabe.

A lissafin da Atiku ya bayar a matsayin shaida a gaban Kotun Daukaka Karar Zabe, sun nuna kenan dukka gaba dayan kuri’un da aka tantance kakaf a jihohi 33, an jefa su ga Buhari da kuma Atiku kenan.

Tazgaro da rashin tabbas din ikirarin da Atiku ya yi, ya kara fitowa fili ne idan aka yi la’akari da cewa an samu kuri’un da aka soke sama da miliyan 1.2 a zaban na shugaban kasa.

Atiku dai yace ya bai wa Buhari tazarar kuri’u miliyan 1.6 a zaben shugaban kasa.

Dalili na hudu na raunin hujjojin da Atiku ya gabatar, cewa shi ya samu kuri’a milyan 18,356,732, Buhari kuma ya samu milyan 16,741,430, shi ne babu lissafin kuri’un Jihar Ribas a ciki.

LISSAFIN-DAWAKAN-RANON ATIKU

Adadin kuri’un da Atiku ya ce ya samu da wanda ya ce Buhari ya samu, yawan su idan an hada aka kwatanta su da adadin wadanda INEC ta nuna sun yi zabe, to a jihohi 33 kenan babu wani dan takara ko wata jam’iyya daga cikin sauran jam’iyyu 71 da suka samu ko da kuri’a daya tal.

Wannan fa idan aka yi la’akari da yawan kuri’un da Atiku ya ce su ya samu, da wadanda ya ce Buhari ya samu, ba wanda INEC ta bayyana ba.

A jihohin Bauchi, Abia da Cross Rivers, lissafin Atiku ya nuna kenan shi da Buhari sun samu kuri’u fiye da wadanda INEC ta tantance a ranar da aka gudanar da zaben na shugaban kasa.

INDA ATIKU YA KWAFSA

A sakamakon da INEC ta fitar na zaben shugaban kasa, ya nuna cewa dukkan jam’iyyun da suka shiga takara su 73, sai da kowace ta samu kuri’u.

Sakamakon ya nuna cewa sauran jam’iyyu 71, idan ka debe APC da PDP, su sun samu jimillar kuri’u 869,758.

Felix Nicholas na jam’iyyar PCP, wanda shi ne ya zo na uku, ya tashi da kuri’u 110,195.

Obadia Mailafiya na jam’iyyar ADC, ya samu kuri’u 97,874.

Shi kuma Gbor Terwase da ya zo na hudu, ya samu kuri’u 66,851.

A BAJE SU A FAIFAI

A jihar Adamawa, inda Atiku ya fito, inda INEC ta ce Atiku ya samu kuri’u 412,266, shi kuma Buhari ya samu 377,488.

Amma shi kuma Atiku ya ce ya samu kuri’a 646,080 daga cikin kuri’u 815,680 din da INEC ta tantance a ranar zabe. Ya ce Buhari ya samu kuri’u 161,600, kamar yadda adadin da ya ce ya leko haka ya ke a rubuce a cikin Rumbun Na’urar adana Sakamakon Zaben INEC.

Wanda duk ya gasganta Atiku, to ya na nufin su biyu kacal suka tashi da dukkan kuri’un da aka jefa a Jihar Adamawa kenan.

Haka abin ya ke a jihohin Akwa-Ibom da Enugu da Sokoto da Taraba. Jihar Zamfara ita ma kamar wadannan jihohi da Adamawa, haka na ta lissafin ya ke.

Wato idan za a yi la’akari da adadin da kuri’un da Atiku ke ikirarin ya samu, to sauran ‘yan takarar shugaban kasa ba su samu ko daya ba kenan.

Duk wanda ya yarda da ikirarin Atiku, to ya na nufin sauran jam’iyyu ba su samu ko da kuri’a daya ba kenan, idan aka yi la’akari da kuri’un da Atiku ya ce ya samu, da wadanda ya ce su ne Buhari ya samu.

Haka nan kuma Abin ya ke a Barno, Benuwai, Bayelsa sauran jihohi da dama.

Share.

game da Author