TAMBAYA: Shin laifine mutum yayi buki don zagayowar ranar Haihuwar sa, ko bukin ranar Masoya ko na sabon Shekara?
AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugaban mu Annabi Muhammad SAW. A cikin fatawar malamai na binciken ilimi na duniya, an tabbatar da rashin halaccin bukin zagayowar ranar Haihuwa (birth Day), da bukin ranar Masoya (Valentine) da na sabuwar Shekara (New Year) Fatawar ta kara dacewa. Baya hallata ga musulmi yin bukukuwan bidi’ah, da yin murnansu, bai dace da musulmi ya yi tarayya da masu yin bukin, ko ya tayasu murna. Fatawar ta ce yin haka taimakawa ne cikin sabo da habbaka shi a bayan kasa. Kuma hakan laifi ne.
Kebe wata rana ta musamman domin bukin zagayowar ranar Haihuwa, da bukin ranar Masoya da na sabuwar Shekara bidi’a ne kuma al’ada ce da dabi’ar mutanen da ba musulmai ba, don haka musulmi ya guji wadannan bukukuwa da murna a ranakun. Wajibi ne musulmi ya dauki wadannan
ranaku kamar sauran kwanaki. Sheikh Islam Ibn Taimiyya ya yi Karin haske akan wadannan bukukuwa kamar haka:
1) Musulmai su kiyaye bin tafarkin kafirci kamar tarayya da su cikin bukukuwa, da halartar bukukuwan.
2) Bai halatta musulmi ya taimaka a wajen yin wadannan bukukuwa ta kowace irin hanya, kamar bada kyauta, sakon taya murna.
3) Bai halatta ga ‘yan kasuwa siya da siyar da abubuwan da ake amfani da su wajen wadannan bukukuwa kamar cakes, da flowers da cards
da dinkuna.
Sheikh al-Islam Ibn Taimiyya da fatawar Lajanal malamai sun haramta bukin zagayowar ranar Haihuwa (Birth Day), da bukin ranar Masoya
(Valentine) da na sabuwar Shekara (New Year), a cewarsu wadannan bukukuwa ne na arna, kuma yin su koyi ne da arna da al-adun arna wadanda suke cinkaro da na musulmi. Sannan kuma suna shagaltar da musulmai da kawar da su akan turba ta kwarai da barnar dukiya.
Wadannan bukukuwa sabon Allah ne da taimako a cikin sabon sa wanda Allah ya hana.
Allah she ne mafi sani.