Idan ba a manta ba jihohi shida ne cikin jihohin da aka yi zabe ba a kammala zabukan su ba. Babban dalili kuwa shine ganin yadda aka samu yawan kuri’un da aka soke a wurare da dama.
Jihohin sun hada da Jihar Bauchi da PDP ce ke kan gaba da yawan kuri’u, Jihar Kano da itama PDP ce ke kan gaba, sai Jihar Filato, Jihar Adamawa, Jihar Sokoto, da jihar Benuwai
Hukumar zabe ta bayyana ranar 23 ga watan Maris a matsayin ranar da za a kammala zabuka a wadannan jihohi.
Kano:
A Sakamakon da aka bayyana, Dan takaran gwamna na Jam’iyyar PDP Abba Yusuf ne ya lashe Zaben da kuri’u 1,014,474, shi ko gwamna mai ci Abdullahi Ganduje ya samu kuri’u 987,819.
Kuri’u 26,655 Abba yafi Ganduje da su.
Sannan kuma an lalata kuri’u 141,694 Wanda a dalilin haka yasa dole sai anyi Zabe a kananan hukumomi 22 da aka samu matsala da kuri’un su.
Sokoto:
Farfesa Fatima wadda itace Shugabar Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, ta ce Gwamna Tambuwal ya samun kuri’u 489,558, shi kuma dan takarar APC, Aliyu Ahmad ya samu 486,145.
Ratar da ke tsakanin jam’iyyun biyu ita ce kuri’u 3, 413 kacal.
Ta ce a cikin kananan hukumomi 22 an soke kuri’u a rumfuna 137 wadanda suka kai adadin 75,403.