HATSARI: Dukkan fasinjoji 157 da ke cikin jirgin Ethiopia sun mutu

0

Rahotanni sun tabbatar da afkuwar hatsarin jirgin saman kamfanin Ethiopian Airline, kuma dukkan fasinjoji 157 da ke cikin jirgin an tabbatar da mutuwar su.

Baya ga wannan adadin fasinjoji, akwai kuma matuka da sauran ma’aikatan jirgin su takwas da aka tabbatar da cewa su ma duk mutu.

Gidan Radiyon BBC ya ce jirgin samfurin Boeing 737, ya tashi ne daga Addis Ababa, babban birnin kasar, ya yi hatsari a kan hanyar sa ta zuwa, Nairobi, babban birnin kasar Kenya.

Jirgin ya fadi ne lokacin kadan baya ya tashi ya fara tafiya.

Jami’ai sun ce an gano inda ya fadi, kuma ana maida hankali a wajen.

Ofishin Firayi Ministan kasar ya sanar da hatsarin, kuma ya mika ta’aziyyar sa ga iyalan wadanda suka rasa rayukan su.

“Daya daga cikin jami’an kamfanin jiragen ya ce hadarin ya faru ne wajen 8:42 na safiyar yau Lahadi.

Share.

game da Author