Hanyoyin da za abi don gujewa kamuwa da cutar Asthma

0

Wasu likitoci dake jami’ar Leicester da gidauniyar ‘Air Prom’ sun gano wani magani mai suna ‘Fevipirant’ dake da ingancin rage yawan yaduwar cutar kasa numfashi ‘Asthma’.

Jagoran binciken Chirstopher Brightling ya bayyana cewa har yanzu ba a kammala tantance maganin ba amma sun gudanar da wannan Nazari ne da bincike ne domin sama wa mutanen dake fama da cutar mafita.

Brightling ya bayyana cewa binciken ya nuna cewa mutane 339 na dauke da cutar sannan a awa daya cutar na yin ajalin mutane 1000 a duniya.

Ya ce cutar ya fi yaduwa ne a kasashen dake tasowa saboda matsalolin rashin samun isassun magungunan cutar, tsadar magungunar da rashin ingancin su.

Brightling yace maganin ‘Fevipirant’ na da ingancin hana cutar kashe cutar da zai sa a samu raguwar yawan zuwa asibiti domin neman magani.

Ya kuma ce maganin na da ingancin rage yawan shan wasu magunguna kamar su ‘Steroids’ da mutanen dake fama da cutar ke yawan yi.

Cutar Asthma cuta ce dake kama manufashin mutum inda a dalilin haka ake samun matsalar rashin mumfashi yadda ya kamata.

Alamun cutar sun hada da ciwon kirji, rashin yin numfashi yadda ya kamata,tari da sauran su.

Shakar gurbatacciyyar iska, hayaki, yawan shan magunguna kamar su Aspirin,Ibuprofen,Naproxen da sauran su, damuwa,tsoro na cikin hanyoyin da ke sa a kamu da Asthma.

Hanyoyin guje wa kamuwa da Asthma

1. Zama cikin tsaftattacen wuri

2. Gujewa yawan shan magunguna ba tare da izinin likita ba.

3. Gujewa shakar gubataciyyar iska, kura da hayaki.

4. Shan maganin da ya kamata da zaran an kamu da mura.

5. A daina yawan damuwa.

Share.

game da Author