Gwamnati za ta kara harajin ‘VAT’ domin biyan karin albashi

0

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa za ta kara kudin harajin ‘VAT’ daga kashi 5 bisa 100 na ciniki zuwa kashi 7.5, domin ta haka ne kawai za ta iya rika tatsar kudade daga jama’a, wadanda za ta rika biyan ma’aikata na karin albashin da aka yi.

Ministan Kasafin Kudi da Tsare-tsaren Tattalin Arzikin Kasa, Udo Udoma ne ya bayyana haka jiya Talata a Abuja.

Ministan y ace tuni dama Shugaban Hukumar Tara Kudaden Shiga Babatunde Fowler ya bayyana hakan, inda ya ce hukumar sa za ta kirkiro hanyoyin da za a tatsi kudade domin biyar karinn abashin.

Udo Udoma da Fowler na da daga cikin manyan jami’an gwamnati da suka bayyana a gaban Kwamitin Kula da Harkokin Kudade na Majalisar Dattawa, a karkashin shugabancin SANATA John Enoh.

A jiya Talata ne Majalisar Dattawa ta yi wa kudirin dokar karin albashi karatun tantancewa na uku.

Dama kuma Majalisar Tarayya ta rigaya ta mika wa Shugaba Buhari kudirin dokar karin albashin, wanda aka amince yin kari daga naira 18,000 mafi kankantar albashi, zuwa naira 30,000 a kowane wata.

Karin zai shafi kudaden shigar kamfanoni da kuma ribar da ake samu a harkokin da suka jibinci fetur da dangogin sa.

“Za mu kara harajin VAT. Duk wanda ya je kasar Ghana ko wasu kasashe a Afrika, zai san cewa harajin mu na VAT bai kai na su yaw aba. Don haka mu ma za mu yi karin harajin kamfanoni da fetur da dangogin sa.

“Abin ya zame mana gaba-kura-baya-damisa. Maganar gaskiya albashin naira 18,000 ya yi wa karamin ma’aikaci kadan a rayuwar sa. Sannan kuma idan ba a kara harajin nan na VAT ba, to gwamnati ba za ta iya biyan karin albashin da aka yi zuwa naira 30,000 a matsayin mafi kamkantar albashi ba.

Share.

game da Author