Gwamna Abdul’aziz Yari na Jihar Zamfara, ya gana da Shugaba Muhammadu Buhari, inda ya yi kururuwa dangane da yadda mahara a jihar sa suke ta kara tanadar makaman da suke ci gaba da kisan jama’a, kona kauyuka tare da yin garkuwa da jama’a.
Yari ya sanar da haka a lokacin da ya ke tattaunawa da manema labarai a Fadar Shugaban Kasa, jim kadan bayan ganawar sa da Buhari, inda ya yi masa karin bayanin halin da jihar ke ciki a hanlin yanzu.
Gwamna Yari ya ce ba zai sake shirya wani zaman sasantawa da masu garkuwa da kisan mutane a jihar ba.
“Na shaida wa jama’a ta cewa har na kammala wa’adi na ba zan sake yin zaman sulhu da mahara wadanda suka addabi jihar mu ba. Saboda na yi haka har sau uku a baya, amma zaman sulhun bai tsinana amfanin komai ba.
“Misali, a zaman sulhun da aka yi na farko, sun gayyaci wasu jami’an mu, sojoji, ’yan sanda, DSS da kuma babban jami’in tsaro na. Sannan kuma an gayyaci wakilan sarakunan gargajiya.
“Mun ga irin shirgin muggan makaman da suke da shi, wanda jami’an tsaron jihar Zamfara ba su ma da irin kwatankwacin su.
“A cikin rumbun ajiyar su daya kawai mun ga sama da AK 47 sun fi 500.
“Kai saboda rainin wayo ma har kyale tawagar mu suka yi suka dauki hotunan tulin makaman da suke da su.
“Amma da muka ce to a zauna a yi zaman sulhu, su mika makaman su, mu kuma mu yi musu afuwa, sai suka ki amincewa.
“To ina tabbatar muku da cewa tun daga waccan rana zuwa yau, har yau ba mu karbi AK 47 guda 90 a hannun su ba.
“Saboda tsabar yaudara, a cikin rani sai suka nemi a yi zaman sulhu, saboda sun san cewa jami’an tsaro za su iya cim masu a duk inda suke, tunda babu sauran wuraren da za su buya.
“Amma da damina ta zagayo, ciyayi da tsirrai suka fito, har suka samu wuraren buya, sai suka ci gaba da hare-haren da suke kaiwa.
Yari ya ce idan ba karfin sojoji aka yi amfani da shi ba, to ba za a iya murkushe maharan da suka addabi jihar Zamfara ba.
Ya kara da cewa kwanan nan za a kara loda manyan makamai zuwa Zamfara domin a yi ta ta kare da mahara a jihar.