Gobara ta babbake ofishin hukumar zabe dake jihar Akwa Ibom

0

Gobara ta kama a ofishin hukumar zabe dake jihar Akwa Ibon ranar jajibirin zabe.

Wani mai gaidin dake aiki a ofishin ya sanar wa PREMIUM TIMES ranar Juma’a cewa gobarar ta tashi ne tun daga karfe biyun daren Juma’a.

” Muna zaune sai muka ji karan fashewar wani abu daga cikin ofishin inda bayan mun duba ne muka ga gobara ce ta tashi.

” Ko da yake mun nemi dauki sannan mun yi kokarin kashe gobarar amma Ina bai yiwu ba.

Wakilin gidan jaridar ya gani wa idon sa yadda gobarar ta babbake ofishin sannan na’urar tattace katin zabe da dama na cikin kayan da suka kone.

Share.

game da Author