Jam’iyyar APC ta bayyana cewa furucin da Atiku Abubakar dan takarar jam’iyyar PDP a zaben shugaban kasa da kuma ita kan ta PDP ke yi, cewa sun ci zabe, ba wani abu ba ne, sai gigitar faduwa zabe.
Kakakin Yada Labarai na Jam’iyyar APC, Lanre Issa-Onilu, shi ne ya furta haka jiya Laraba, inda ya ce zafin kayen zaben da PDP ta sha har yau ba ta dawo cikin hayyacin ta ba, shi ya sa jam’iyyar da dan takarar ta ke ta sambatun cewa sun ci zabe.
Tuni dai Atiku Abubakar da jm’iyyar PDP sun ki amincewa da sakamakon zaben, sun kuma garzaya kotu.
Atiku ya yi ikirarin cewa rumbun na’urar INEC mai tattara sakamakon zabe ya nuna PDP ce ta yi rinjaye a kan APC da kuri’u miliyan 1.6.
Wannan bayanin na kunshe ne a cikin wani kundi mai dauke da shafuka 139 da Atiku ya bayyana yadda aka murye zaben shugaban kasa.
Sannan kuma ya ce ya na da tulin hujjojin da suka tabbatar da zai kayar da Buhari a kotu.

Atiku ya gabatar wa Kotun Daukaka Kara kundin hujjojin sa na samun nasara da kuma hujjojin an murde zabe, har guda 50.
Sai dai kuma jam’iyyar APC ta ce duk gigitar faduwa zabe ce ke damun PDP da kuma mafarki daga barci mai nauyin da jam’iyyar ta yi.
APC ta kara da cewa tun daga ranar da aka bayyana cewa Atiku ya fadi zabe, bai kara samun sukunin zama wuri daya ba, sai ragaita ya ke yi, ya je nan, ya je can ya na ta zubar da surutai na mai kama da wanda gigitar faduwa zabe ta kidimar da shi.
Ta ce zargin da Atiku ya yi wa INEC cewa rumbun na’urar ajiyar sakamakon zaben ta ya nuna Atiku ne ke kan gaba da kuri’u milyan 1.6, hakan inji APC ya na da barazana sosai, domin ya nuna Atiku da PDP su na da wani boyayyen shiri a kan INEC.