Gidauniya ta yi wa mutane gwajin cutar Koda kyauta a Abuja

0

A makon da ta gabata ne gidauniyar ‘Omotayo Kidney Care’ ta yi wa mutane gwajin cutar koda kyauta a Abuja da kuma wayar da kan mutane game da cutar sannan da hanyoyin gujewa kamuwa da ita.

Shugaban gidauniyar Omotayo Akinrinde ta sanar da haka sannan ta kara da cewa wayar da kan mutane game da cutar ya zama dole ganin cewa cutar na cikin cututtukan dake kisa matuka a duniya.

Ana iya kamuwa da wannan cutar ne idan ana yawan shan magunguna musamman magungunan gargajiya da shan kwayoyi ba tare da izinin likita ba, rashin motsa jiki sannan kamuwa da cutar hawan jini, tarin fuka, kanjamau da sauran su na iya haddasa wannan cuta.

Alamun cutar sun hada da yawan yin ciwon kai, kumburin jiki musamman kafafuwa da sauran su.

” Gidauniyar Omotayo Kidney Care ya fara wayar da kan mutane ne a watan Nuwamba 2017 a shafin mu ta Facebook dake yanar gizo inda muka yi kokarin fadakar da mutane game da yadda za su iya guje wa kamuwa da wannan cuta.

Akinrinde ta ce yin wannan gwajin zai taimaka wa mutane wajen sanin matsayin su game da wannan cuta.

Akinrinde ta yi kira ga mutane da su rika shan ruwa, cin ‘ya’yan itatuwa musamman tufa, guje wa yawan shan magunguna, guje wa shan giya da taba, motsa jiki domin guje wa kamuwa da cutar koda.

Wani cikin mutanen da wannan gidauniyar ta yi wa gwaji Abdulkaheem Abdulsalami ya jinjina wa aiyukkan wannan gidauniyar.

Share.

game da Author