Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta bayyana cewa sakamakon zaben gwamna da aka gudanar a Jihar Filato bai kammala ba.
Babban Jami’in Zaben Jihar, kuma Shugaban Jami’ar Jihar Benuwai, Farfesa Richard Kimbir ne ya yi wannan sanarwa da karfe 3:13 na dare.
Ya ce tilas sai an samu ratar da za ta tabbatar da cewa kuri’un da aka jefa sun yi daidai da ratar da jam’iyyu biyun da suka fi samun kuri’u ta nuna.
Gwamna Lalong na APC ya samu kuri’u 583,255, shi kuma Jeremiah Useni na PDP ya samu 538,326.
INEC ta ce bambancin da ke tsakanin APC da PDP kuri’a 44,929 ce, alhali kuma kuri’u 49,377 ne aka soke.
A kan haka ne ya ce INEC za ta sake zabe a kananan hukumomi 13 daga cikin 17.
Inda za a sake zaben sun hada da: Jos ta Arewa, Jos ta Kudu, Kanam, Langtang North, Langtang South, Mangu, Panshin, Kanke, Mikang, Quanpan, Riyom, Shendam, da Wase.
Ya ce wani wani dalilin soke wasu sakamakon shi ne aringizon kuri’u da kuma kin yin amfani da ‘card reader’ da aka yi a wasu wurare.