Gwamnan jihar Kaduna ya kwankwadi ruwan Kuri’u a mazabar sa na unguwar Sarkin musulmi, Kaduna.
A sakamakon zaben da aka bayyana, El-Rufai ya samu nasarar lashe kusan duka kuri’un da aka kada a wannan mazaba.
El-Rufai ya tashi da kuri’u 367 inda shi kuma dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP, wato Isah Ashiru ya samu kuri’u 59 kacal.
Haka nan shima Isah Ashiru ya yi wuji-wuji da gwamna Nasir El-Rufai a mazabar sa dake Kofar Fada, a garin Kudan.
Isa Ashiru ya samu kuri’u 283 inda El-Rufai ya samu kuri’u 33.
Har yanzu ana tattara kuri’u a Kaduna.