DANKARI: Jam’iyyar APC ta dakatar da gwamna Amosun da Okorocha daga jam’iyyar

0

Kakakin Jam’iyyar APC, Lanre Issa-Onilu ya bayyana wa manema labarai cikin takarda da ya fitar da yamman Juma’ar nan daga hedikwatar jam’iyyar APC cewa jam’iyyar ta dakatar da gwamnan Jihar Ogun Ibikunle Amosun da gwamnan Jihar Imo, Rochas Okorocha daga jam’iyyar.

Duk da cewa jam’iyyar APC din ta dakatar wadannan gwamnoni, ta mika takardar neman a kore su kwata-kwata daga jam’iyyar ga kwamitin gudanarwar jam’iyyar.

Idan dai ba a manta ba, da Amosun da Okorocha duk suna mara ma wata jam’iyya ce baya a zaben gwamna mai zuwa ba APC ba.

Jam’iyyar bata dauka wannan huklunci ba sai bayan da lashe zaben shugaban kasa.

Share.

game da Author