Dan fashi ya ce ‘yan sanda suka tilasta shi kulla wa Saraki sharri

0

Daya daga cikin wadanda ake zargi da hannu a fashin banki da aka yi a Offa, cikin Jihar Kwara cikin 2018, ya zargi ‘yan sanda da tilasta shi cewa akwai hannun Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki a cikin fashin.

Wanda ake zargin mai suna Friday Ankininibosin, ya bayyana haka ne a Babbar Kotun Ilorin da ke Jihar Kwara a jiya Juma’a.

Kafofin yada labarai da dama ciki har da Nigerian Tribune sun ruwaito wannan labari daga kotun.

Akininibosun da wasu mutane biyar su na fuskantar tuhumar aikata laifin fashi da makami wanda ya yi sanadiyyar kashe jama’a da dama, ciki har da ‘yan sanda da yawa.

Ya shaida wa kotu cewa shi fa tun da ya ke a duniya bai ma taba ganin Saraki ido da ido ba.

Akininibosun ya ce wani tsohon dan sanda da ke da hannu a cikin fashin, an kashe shi ne saboda ya ki yarda ya goga wa Saraki kashi-kajin sharrin hannu a cfashi da makami.

Fashin wanda aka yi a First Bank, a ranar 5 Ga Afrilu, 2018, ya ci rayuka 17, ciki har da na ‘yan sanda tara.

Bayan kama ‘yan fashin ne ‘yan sandan Najeriya suka ce wasu da aka bincika sun ce akwai hannun Bukola Saraki a fashin.

‘Yan sanda sun ce wadanda suka yi fashin ‘yan bangar siyasar Saraki ne, kuma shi ne ke bas u makamai da harsasai.

Tuni dai Saraki ya karyata wannan zargi, ya ce bi-ta-da-kullin siyasa ne kawai ake yi masa.

Kallo ya koma sama jiya Juma’a a Babbar Kotun Ilorin, inda Akininibosin ya janye furucin da ya yi wa ‘yan sanda a baya cewa da hannun Saraki a fashin.

Ya ce sharri ne, kuma ‘yan sanda ne suka tilasta shi ya kulla wa Saraki.
Ya ce gaskiyar magana ‘yan sanda ne suka tilasta shi cewa ya saka sunan Saraki a cikin fashin.

Sannan kuma ya shaida wa alkali cewa bayanin da ke a rubuce cewa ya ce da hannun Saraki a fashin, ba shi Akininibosin din ne ya rubuta shi da hannun sa ba, wani dan sanda ne ya rubuta bayanan wai a madadin sa.

YADDA ’YAN SANDA SUKA SA NA KULLA WA SARAKI SHARRI

“Sun kama ni, suka bankara hannaye na ta baya, sannan suka kamo kafafuwa na suka bankare su ta baya suka hada da hannayen suka daure. Aka rataye ni a bisa wani dogon rodi. An gicciye rodin a kan tebura guda biyu.

“Daga nan wani babban jami’in ‘yan sanda mai suna Abba Kyari ya shigo, ya ce min na ce Shugaban Majalisar Dattawa ne ya ba mu bindigogin da muka yi fashi a bankunan Offa.” Haka jaridar NigerianTribune ta wallafa, inji Akininibosin a gaban mai shari’a, jiya Juma’a a Ilorin.

“Na shaida wa Abba Kyari cewa rayuwa ta na cikin hatsari, ba zan iya fadin haka ba. daga nan ya ce ai su zan yi wa wannan bayanin, daga nan kuma za su biya ni, sannan za su sake ni. Duk da haka na ki amincewa. Daga nan suka ciccibe ni suka sake maida ni suka kulle, domin a lokacin ko takawa ma ba na iyawa da kafafu na saboda tsananin azabtarwa.

Abba Kyari ne jami’in dan sandan da ya yi jagorancin kamo wadanda ake zargi da yin fashin.

An sha zargin Kyari da laifin tauye hakkin dan Adam da kuma tsoma hannu cikin dagwalon harkallar kudade. Amma duk ya na karyatawa.

Har ila yau, Tribune ta kara ruwaito cewa Akininibosin ya shaida wa kotu cewa ‘yan sanda sun kashe mutane biyar a gaban su, domin su kara razana su.

Sannan kuma suka tilasta su kwantawa a kan gawarwakin wadanda suka harbe din.

“Sun harbe ni a kafafuwa na biyu. Daga nan aka dauke ni aka kai ni ofishin Abba Kyari. A can ya tambaye ni ko na shirya ba su hadin kai na yi abin da suke so? Ni kuma da na ga halin da na ke ciki, sai na ce masa na amince, kuma na roke kada ya kashe ni.

“Washegari sai aka kawo Michael Adikwu domin ya shaida mu kuma ya tabbatar da mu din ne, kuma ya yi musu bayanin alakar mu da shi.

A GABA NA ’YAN SANDA SUKA BINDIGE ADIKWU

Adikwu tsohon dan sanda ne. Ya kale mu ya ce bai san mu ba. suka kuwa rufar masa da azabtarwa. Duk da haka ya ce bai san mu ba. Ganin haka sai suka dirka masa bindiga a gaban mu, ya dadi ya mutu.”

‘Yan sanda sunn tabbatar da mutuwar Adikwu a hannun su, amma sun ce ba sanadiyyar azabtarwa ba ce. Ajalin sa ne ya kawo kawo karshe.

Haka kuma jaridar ta ce Akininibosin ya ce an kawo wani dan jarida, wanda ya yi rikodin na bayanan da aka tilasta su kala wa Saraki sharri.

“Tsoro ya kama ni, ina tunanin daga harbe Adikwu, ta kai na za a dawo a dirka min bindiga. Amma zuwa can sai ga wata ‘yar jaridar wani gidan talbijin, ta zo da wani bayani rubuce a takarda. Ta nuna musu ta ce wannan bayanin ne ake so na fada. Idan na ki fada kuma, to za a kashe ni.

“To ka ji yadda aka yi har na amince a gaban wannan ‘yar jarida, na yi furucin da da kulla wa Saraki sharrin cewa shi ya ba su bindigogin da muka je muka yi fashi.”

Akininibusin ya kara da cewa ko a lokacin da aka tilasta shi yin furucin wanda aka yi rikodin, an rika jibgar sa.

Share.

game da Author