DALLA-DALLA: Yadda El-Rufai, Ashiru za su fafata ranar Asabar, mai rabo ka dauka

0

Idan dai akwai wata jiha a Najeriya da kowa ya Kalmashe kafafu sannan an nade hannaye ana jiran sakamakon zaben gwamnan jihar bata wuce jihar Kaduna ba.

Duk da cewa akwai wasu jihohin da ake ganin suma fa za a kai ruwa rana matuka suma a can, jihar Kaduna da ake yi wa lakabi da cibiyar Arewa tafi tsole wa mutane ido.

Ba ya ga haka, gwamnan dake kan mulki a jihar, dan gaban goshin shugaban kasa Muhammadu Buhari ne da kowa ke ganin koda wani a kasar nan ba zai kai labari ba toh, ba gwamna Nasir El-Rufai bane.

Ko ta ko ina sai siyasa kawai ake bugawa babu kakkautawa a jihar. Duk ta inda za abi a samu nasara dukka jam’iyyun biyu da ‘yan takarar suna bi domin ganin sun cira tuta ranar Asabar.

Baya ga kide-kide da zaka ji na wasa ‘yan takara, sai kyaututtuka da zaka ga ana ta rarrabawa da kuma alkawurra da ake ta dauka a tsakanin mutane da yan siyasar jihar ko ta ina a garin Kaduna za kaga hada-hada kawai ake ta yi na yan siyasa.

Isa Ashiru

1 – Shi dai dan takarar gwamnan jihar na jam’iyyar PDP, Isah Ashiru, ana yi masa ganin ba mutum bane mai kazar-kazar da zai iya rike Kaduna yadda ya kamata a matsayinta na cibiyar Arewa har a samu ci gaban da za a iya alfahari da shi.

2 – Har yanzu wasu da yawa na ganin jam’iyyar PDP ta sire wa mutane da ba su yi shirin su dawo da ita ba a jihar.

3 – Taron dangi da ‘yan siyasa suka yi don kada Isa Ashiru na jam’iyyar PDP, da ya hada da canja sheka da wasu ‘yan jam’iyyar suka yi zuwa jam’iyyar APC.

4 – Ana yi masa ganin bai goge ba a harkar karatun boko sannan bashi da wayewa irin ta zamani kamar gwamna mai ci.

5 – Malaman Kaduna sun yi masa ca, wai ya yi alkawarin fifita mutanen yankin kudancin  Kaduna fiye da ‘Yan uwansa na Arewacin Kaduna.

6 – Ana yi masa ganin ba zai iya yin tattali irin yadda gwamna mai ci yake yi ba idan ya dare kujerar mulki, watanda da kuadaden jama’a za a rika yi.

7 – Ba a cika jin duriyarsa akai-akai ba a jihar.

Nasir El-Rufai

1 – Shine gwamna mai ci. Akwai wannan karfi ta gwamnati dake rataye da shi wanda zata iya yi masa tasiri.

Sai dai Kuma yayi matukar sire wa mutanen jihar da har abokanan aikin sa sukan lallaba suna sukar sa a bayan fage.

2 – Ana yi wa El-Rufai lakabi da mutum ne mai taurin kai. Babu wanda ya isa ya bashi shawara ko kuma ya dauki shawarar sa. Hakan ya sa wasu na ganin ba mulki don talakawa ya ke yi ba. Abin da ya ga dama kawai yake yi. Hakan na ba mutane tsoron cewa idan aka sake bashi dama a wannan lokaci da ba zai bukaci mutane ba, ashe an kade.

3 – Koran ma’aikata da yayi zai yi matukar tasiri a wannan zabe. Baya ga korar, wasunsu da dama ba a iya biyan su hakkokin su ba.

4 – Rusa masarautu da yayi. Wannan abu ya yi matukar tada wa mutanen jihar Kaduna hankali musamman mazauna karkara. Mafi yawan su a dan wannan rayuwa ta masarautu suke cin abinci. A wasu garuruwan ya yi sandiyyar tada fitintinu a tsakanin gidajen sarauta.

5 – Watsi da ‘yan siyasa da nada wadanda ba ma ‘yan asalin jihar kaduna bane sannan aka nada su a manyan mukamai a jihar.

6 – Har yanzu ‘yan kasuwa ba su yi na’am da gwamna El-Rufai ba cewa tun barazanar farko da yayi musu na rusa wasu manyan kasuwanni a jihar na nan ba su manta ba. Kila likimo yake musu idan ya zarce, kowa zai dandana kudar sa.

7 – Ba a ga maciji a tsakanin sa da mutanen yankin Kudancin Kaduna, Inda suka lashi takobin kuri’un su ba nashi bane.

Yadda za ta kaya

El-Rufai: Shi dai Nasir El-Rufai gwamnan Kaduna, ya samu yabo matuka musamman a wajen yadda ya jajirce ya toshe kunnuwar sa ya ki biye wa ‘yan ‘bani ka lashe’ ya maida hankali wajen inganta fannin Ilimi a Jihar. Ya kama aikin gyara makarantun Jihar babu kakkautawa da a yanzu haka yawan dalibai yan makaranta ya karu da kusan kashi 100 bisa 100.

2 – Sannan kuma zaban mataimakiya , Hadiza Balarabe, musulma wanda ba a taba yi ba ya dada kara masa farin jini a Jihar musamman ga musulmai.

3 – Da yawa na ganin shine wanda zai iya rike Kaduna ba tare da ana yi masa katsalandan ba a harkokin sa ko kuma ace wai wani ubangida ya zame masa kashin kifi a wuya.

Isah Ashiru:

1 – Da walakin a karon farko a jihar Kaduna za a wancakalar da gwamnati mai mulki.

Isah Ashiru ya zabi ya kame bakin sa ne yayi shiru tsit, ya bi jama’a yana neman kuri’un su.

2 – Wasu da dama basu san irin gogewar sa a siyasa da kuma mulki Ba domin fitaccen dan siyasa ne kuma tsohon ma’aikacin gwamnati.

3 – Baya ga dubban kuri’u da zai samu a kudancin Kaduna, Isa dan asalin garin Kudan ne, bazazzagi sannan basarake. Ka da a manta akwai dubban magoya bayan sa a wannan yanki da zai yi masa tasiri a zaben.

Wannan hasashe ne da wakilin PREMIUM TIMES HAUSA ya yi bayan jin ra’ayoyin mazauna jihar Kaduna.

Share.

game da Author