Dalilin da ya sa ake damawa da mu a lokuttan zabe – Rundunar sojin Najeriya

0

Rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa dalilin da ya sa dakarun ta ke tsoma kai a harkar zabe shine don hada kai da rundunar ‘yan sanda domin samar da tsaro a lokuttan zabe.

Rundunar tace dokar kasa ta ba su damar yin haka shine ya sa ake damawada su a samar da tsaro a lokacin zabe.

Jami’in rundunar Onyema Nwachukwu ya sanar da haka wa manema labarai ranar Juma’a inda ya kara da cewa rundunar za ta gudanar da aiyukanta na samar da tsaro bisa ga tsarin doka kasa.

Ya kuma ce rundunar ta amince wa sojojin da suke da za su iya jefa kuri’a su yi haka ba tare da sun saka rigar su ta aiki ba.

‘‘Sojojin da suke aiki ranar zabe za su samar da tsaro, su kama duk sojan da ya nufi rumfar zabe da rigar aiki domin kada kuri’a da kama duk wanda bashi da alaka da jami’an tsaro kuma yake sanye da rigar su ta aiki a ranar zabe.

Ya kuma yi wa iyalen sojojin da aka kashe ta’aziya yana mai cewa duk wani ran dan Najeriya na da matukar mahimmanci wa kasar gaba daya.

Share.

game da Author