Duniyar kwallon kafa a yanzu kowa ya san ta na damawa da kungiyar Liverpool. Hatsabiban ‘yan wasan ta uku, Mohamed Salah, Sadio Mane da Faminho sun fitini Ingila da Turai a kakar wasan Firimiya da gasar Champions League na shekarar da ta gabata.
Duk da cewa Liverpool a wannan kakar da mu ke ciki ba ta kai zafin kakar bara ba, har yanzu dai za a iya cewa zaki dai zakin ne.
Ba don Real Madrid ta taka mata burki a gasar bara ba, da za a iya cewa a yanzu Liverpool ce ke rike da kofi.
Kafin ta kai ga zagaye na uku a kakar bara, sai da ta yi raga-raga da kungiyar Roma har gida a birnin Rome.
Don haka kociya Jurgen Klopp da kungiyar sa ba za su ji tsoron wata wai ita FC Porto ba.
A wannan kakar ta bana kuwa, FC Porto din ce ta fitar da Roma kafin daga baya aka hada ta kafsawa da Liverpool din.
Akwai tsoffin kuraye a cikin Porto, ko ma a ce tsoffin mayu wadanda sun ci dubu sai ceto. Sai dai kuma a gaskiya, duk sun zama tsoffin kuraye masu wawura daga zaune. Amma ba kasafai suke iya bi a guje su farauto su ci ba.
Iker Casillas da Pepe dukkan su tsoffin ’yan wasan Real Madrid ne da duk duniya ta san su. Ga kuma Hector Herrera. Amma fa a sani ba sunan ka ne zai iya kai kungiya kamar Liverpool a kasa ba. Sai idan ka iya kwallo. Ka tabbatar ka jefa mata kwallo a raga, sannan kuma ka hana ta jefa maka. Maganar gaskiya kenan.
Kocin FC Porto ya san akwai aiki a gaban sa, aikin ma kuma ja-wur. Ba kowane dan wasa ke iya keta mai tsaron bayan Liverpool ba, wato Virgil van Dijk. Ga dai karfi, kuma ga iyawa.
‘Yan wasan gaban Liverpool su ne abin tsoro sosai. Idan ka tare Faminho, to yaya za ka yi da gajere-kusar-yaki, Sadio Mane? Ko kuwa tsaye za ku yi galala har Salah ya yi ta zabga muku sakiyar da babu ruwa?
i ba, ko kadan.
Discussion about this post