Bulkachuwa ta hori alkalan kararrakin zabe kada su yi hukuncin son rai ko tsoro

0

Shugabar Kotun Daukaka Kara, Zainab Bulkachuwa, ta hori alkalan da za su gudanar da shari’un da suka danganci kararrakin zabe da cewa su tabbatar sun kauce wa yanke hukunci na son rai, kuma kada su yi hukunci a bisa tsoron wani bangare.

Bulkachuwa ta yi wannan gargadin ne a jiya Laraba wurin da ta gana da masu shari’ar, a Abuja.

Bulkachuwa ta kaddamar da kotun kafin Babban Mai Shari’a na Riko Tanko Muhammad ya rantsar da su.

Ta hore su da su kasance su ke rike da kotun su, kuma hukunci a hannun su ya ke, ba tare da wani ya karkatar da akalar su ko nuna bangaranci ko tsoron wani ba.

Ta ce duk wanda cikakkun shaidu suka tabbatar da cewa shi ne ya yi nasara, to a ba shi nasarar sa, a ba wanda ya fadi rashin nasarar sa.

Ta kuma ja hankalin su dangane da irin gagarimin aikin da ke gaban su. Don haka sai ta ce su tabbatar sun jajirce wa aiki tukuru, tare kuma da nuna kwarewa wajen yanke hukkuncin su.

“A matsayin mu na masu shari’a, kada mu sa son-zuciya, shakku, tsoro, tausayi ko kullatar wani tsakanin wanda ake kara ko wanda ya yi kara. Mu kasance mu na yin hukuncin da doka ta tanadar.”

Alkalan dai su 250 ne, an yi musu wannan gargadin ne a Babbar Kotun Tarayya da ke Gundumar Gudu, Abuja.

Share.

game da Author