Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi tir da harin da aka kai a karamar hukumar Sanga dake jihar Kaduna.
Buhari ya ce babu wani shugaba da zai kwantawa barci hankalin sa kwance bayan mutanen sa na fama da matsalar hare-haren ‘yan ta’adda ba.
Akalla mutane 10 ne aka kashe a wannan hari.
” Irin wadannan mutane da ke aikata irin wannan ta’asa ba su da tunanin mutane a zuciyar su.
” Duk da cewa gwamnati ta na kokarin ganin an kawo karshen wannan abin tashin hankali dole ne sai suma mutane sun hada kai da gwamnati wajen gani an kawo karshen haka.
Buhari ya koka da yadda aka maida komai siyasa a kasarnan har da rayukan mutane ba a dauke shi da daraja ba ” Da zarar ana kokarin bankado irin wadannan mutane masu zuga matasa sai ayi wa gwamnati caaa, cewa wai ba za a tuhumi na su ba.
” Kiyayya da mutane suka saka a zukatan su ga juna da laka wa wani bangare da ba na su ba laifin matsalar shine babban dalilin da ya sa ba a iya gano farko ballantana yadda za a iya kawo karshen wannan matsala.
Baya ga wannan hari da aka kai a Karamar hukumar Sanga, Karamar hukumar Kajuru ma suna fama da irin wadannan hare-hare domin a ‘yan kwanakin nan ma sai da aka rika kai hari kauyukan karamar hukumar Kajuru.
Baya ga irin wadannan hare-hare, kauyuka Birnin Gwari ma na fama da ayyukan mahara da masu garkuwa.
Discussion about this post