BUHARI, ATIKU A KOTU: An ba APC damar binciken kayan zaben 2019

0

Kotu ta amince kuma ta bai wa Jam’iyyar APC damar da ta bai wa PDP, cewa ita ma za ta iya binciken kayan da aka gudanar da zaben 2019 na shugaban kasa da su.

Farkon watan Maris ne PDP da dan takarar zaben shugaban kasa na jam’iyyar, Atiku Abubakar suka garzaya kotu domin neman iznin a ba su damar binciken takardun zaben shugaban kasa da aka gudanar a fadin kasar nan.

Kotun kuwa tun a ranar da aka shigar ta rokon, ta amsa wa PDP da Atiku cewa an ba su dama.

Sai dai abin da kotu ba ta amince ba shi ne roko na biyu da Atiku da PDP suka yi cewa su na so a ba su damar yi wa wasu bayanan sirrin zaben bincike na kwakwaf ta hanyar yin amfani da na’urori.

Wannan ne kotu ta ce babu hurumin yin haka a tsarin zaben Najeriya.

Ganin haka ne ita ma APC ta nemi a amince mata domin ta binciki kwafe-kwafen takarsun sakamakon zaben, kamar yadda aka bai wa PDP dama.

Mataimakin Mashawarcin APC a kan al’amurran da suka shafi kotu, Yusuf Mamman ya tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa kotu ta bada wannan dama kamar yadda APC din ta nema.

Majiyoyi da dama daga Babbar Kotun Daukaka Kara a Abuja sun tabbatar da cewa a ranar Alhamis Babban Mai Shari’a Abdul Aboki tare da wasu Manyan Alkalai biyu, sun zauna sun duba, kuma sun bai wa APC wannan dama da ta nema.

Majiyar ta ce kwafen takarda biyu ne APC suka aika wa kotun, wato daya na Shugaba Muhammadu Buhari, a matsayin san a dan takarar APC, daya kuma na APC din ita kan ta, a matsayin ta na jam’iyya.

Atiku ya ce zai yi binciken takardun zabe domin ya shirya maka INEC da jam’iyyarv APC kotu, a kana bin da ya kira harkalla, zamba, murdiyya da magudin zaben da aka yi masa a zaben da aka gudanar ranar 23 Ga Fabrairu.

Share.

game da Author