A tunanin dukkan ‘yan Najeriya, kusan kowa ya sa rai cewa Bola Ahmed Tinubu, wanda ake wa kallon cewa shi ne jagoran jam’iyyar APC, zai yi namijin kokarin ganin cewa jihar sa ta asali, wato Lagos ta yi abin kwarai wajen tula wa APC da Shugaba Muhammadub Buhari tulin kuri’u a wannan zabe da ya gabata.
Ba don komai ba sai don ganin cewa bangaren su ne ke zuba ido da kuma sa rai cewa zai fitar da dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, bayan Buhari ya kammala wa’adin zango na biyu.
Baya ga wannan kuma, Lagos a can ne mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya fito shi da minista Fashola.
Da dama kuma na ganin cewa Lagos ce ta fi sauran jihohin kasar nan cin moriyar gwamnatin Buhari.
A maimakon a ce APC ta samu tulin kuri’u masu yawa daga Lagos, sai gani aka yi APC da PDP na neman yin kankankan a Legas.
Tambayar da mutane suka rika yi, shin ko dai alkadarin siyasar Tinubu ya kusa karyewa ne, wato ya gama hawa saura gangara kenan?
A ranar jajibirin zabe, an nuno wasu suntuma-suntuman motocin banki guda biyu su na shiga cikin gidan Tinubu da yammacin Juma’a, kwana daya kafin zabe.
An rika yayata cewa motocin biyu damfare suke da makudan kudaden da shi Tinubu din zai yi amfani da su a dalilin zabe.
Jagoran na APC ya shaida wa kafafen yada labarai cewa e, tabbas kudi ne motocin suka kai masa.
“Ina ruwan mutane don sun ga motocin banki sun shiga da kudi a cikin gida na.
Kudi na ne, ba kudin wasu ba. Kuma ina da ikon karbar kudi na a inda na bayar da ajiyar su. Wanda kuma ke ganin ya na da hakki a cikin kudi na, to ya fito ya yi min bayani.
“Wanda ya damu don ya ga na dauki kudi na daga banki na kawo gida na, to wannan matsalar sa ce, ba matsala ta ba. Shi ta shafa.
“Kudi na ne ba kudin gwamnati ba. Tun da Buhari ya hau mulki ba a taba ba ni kwangila ba ko ta naira daya tal.’ Duk wanda ke tsammanin kudin gwamnati ne, to ya je ya bada shaidar inda gwamnati ta ba ni kudin.” Inji Tinubu.
Duk da cewa Tinubu ya karya dokar safarar kudade ta EFCC da ya fitar da buhunan kudaden kuma babu tartibin kasuwancin da aka yi da su, wannan bai sa EFCC ta bincike shi ba, ballantana a gurfanar da shi.
Jama’a da dama sun yi mamakin yadda EFCC ta kauda kai daga kudaden da Bola Tinubu ya rika jida daga banki ya na kaiwa gida, a ranar jajibirin zabe. A gefe daya kuma sai suka bige su na farautar kananan wasu da ake zargin ‘yan sayen kuri’a ne, har da kamen wasu da aka gani da naira dubu 50,000 a ranar zabe.
Discussion about this post