Hukumar hana yaduwar cutar kanjamau ta kasa (NACA) ta bayyana cewa mutane miliyan 1.9 ne ke dauke da cutar kanjamau a Najeriya.
Shugaban hukumar Sani Aliyu ya bayyana haka cewa bisa ga sakamakon binciken da hukumar ta gudanar a shekarar 2018.
Idan ba a manta ba daga watan Yuli zuwa Disambar 2018 hukumar NACA ta gudanar da binciken domin sanin adadin yawan mutanen dake dauke da cututtukan kanjamau, Hepatitis B da C.
Yin wannan bincike zai taimaka wa gwamnati wajen samar da kula da kuma inganta hanyoyin kawar da cutar daga kasar nan.
Sakamakon binciken ya nuna cewa mutanen dake dauke da cutar kuma masu shekaru 15 zuwa 49 sun kai kashi 1.4 inda daga ciki kashi 1.9 mata ne sannan kashi 0.9 maza.
Sannan adadin yawan mutanen dake dauke da cutar kuma ke samun kula dake da shekaru 15 zuwa 49 sun kashi 42.3 inda daga ciki kashi 45.3 mata ne sannan kashi 34.5 maza.
Binciken ya kuma kara nuna cewa yankin kudu maso kudu ce ta fi samu yawan mutanen dake dauke da cutar a kasar nan inda yawan su sun ya kai kashi 3.1.
A Arewa ta tsakiya mutanen dake dauke da cutar sun kai 0.2, kudu maso gabas kashi 1.9, kudu maso yama kashi 1.1, arewa maso gabas kashi 1.1 sannan arewa maso yamma kashi 0.6.