Duk da cewa an fara zabe lami lafiya a Jihar Bauchi, rincimi ya kaure a rumfar Sanata Abubakar Maikifi, Cresent, da ke Jahun bayan da aka gano cewa an kaekatar da wasukayan zaben wurin zuwa wata runfar zabe da ke makarantar Firamare na Makama.
Rincimin ya tirnike har sai da ta kai ga tawagar Daraktan SSS na Bauchi da Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Bauchi Ali Ganga sun je wurin domin a kwantar wa jama’a hankali.
Shugaban Hukumar Bayar da Ilmin Bai Dayan a Jihar Bauchi, Yahaya Yaro, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa a wannan rumfa ce ya ke jefa kuri’a, amma wasu masu kudirin tauye wa jama’a hakkin jefa kuri’a ne ke da alhakin karkatar da kayan zaben.
Ya ce tun daga zaben 1999jama’a ke jefa kuri’a a rumfar zaben, amma sai wannan zaben ne za a hana su damar su.
Ya ce ko a mako biyu da suka gabata, a wurin suka yi zaben shugaban kasa da na majalisar tarayya.