BARCELONA vs FC LYON: Maganin Biri Karen Bamaguje

0

FC Lyon ta yi karkon kifi a ruwa, yayin da ta je birnin Barcelona aka sheka mata ruwan kwallaye 5:1.

An yi tunanin cewa tunda canjaras aka tashi wasan a birnin Lyon, watakila kungiyar ta Faransa za ta yi jimirin tsayuwar kwamin jaki a yi kare jini, biri jini da ita a Barcelona.

Sai dai kuma tun kafin a tafi hutun rabin lokaci aka zabga mata kwallaye boyu. Hakan ta janyo Lyon cire mai tsaron gidan ta, inda ta musanya shi da wani.

Dawowa daga hutun rabin lokaci kuma ya sa an yi wasan kura da Lyon, inda aka kara mata kwallaye uku cur, ita kuma ta ci daya tal.

Sai dai kuma duk da wannan nasara da Barcelona ta samu, mai sharhin wasanni Craig Burley na ganin cewa da sauran rina a kabar Barcelona, domin sa’ar kungiyar shi ne ta na da masu ci mata kwallaye, amma a gaskiya katangar bayan Barcelona ta na girgiza sosai.

Dalili kenan Burley ya ce Barcelona ta guji ranar kin dillanci.

Share.

game da Author