Jami’an tsaro sun bayar da sanarwar cewa sun cafke wasu ‘yan sanda shida dangane da banka wa wani ofishin Rajista na Yanki mallakar INEC da wasu batagari suka yi a Jihar Ebonyi.
Wadanda aka kama din dai an tura su kula da kayan zabe ne a ofishin da ke Karamar Hukumar Ezza ta Arewa a Jihar Ebonyi.
Wasu batagari sun kai wa ofishin hari wajen karf 2 na dare a ranar zabe, suka kone ofisoshi uku kurmus.
INEC ta ce ofishoshin da aka boye kayan zabe masu matukar muhimmancin ne aka kone.
Rahotanni sun ce an kama jami’an tsaron su shida ne saboda sun kyale batagarin matasan sun kone ofishin.
Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar, Awoshola Awotinde ne ya badar odar kama su, bayan da ya gabatar da Mataimakin Sufeto Janar na Shiyyar.
Ita ma Kakakin Yada Labarai ta ‘Yan Sandan Ebonyi, Loveth Odah, ta tabbatar da kama yan ’yan sandan su shida.
Ta ce kona kayan zaben ya haifar da tsaikon jefa kuri’a ga jama’a sama da 36,000.
Hakan ta sa tilasa aka ce zaben bai kammalu ba.
Ta ce an tura jami’an tsaro na mobal biyu tare da ‘yan sanda hudu a kowace cibiya.
An kuma shaida musu cewa da sun ga wasu alamomin rudani, to su gagauta sanar da hedikwata domin a kai daukin gaggawa.
‘Yan sandan sun shaida cewa batagarin sai da kashe janareta wurin ya yi duhu kafin su banka wa ofishin wuta.