Ba mu da wani uzurin faduwa sauran zabukan da za a sake mamaitawa – Osinbajo

0

Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, ya bayyana cewa babu wani dalilin da zai sa jam’iyyar APC ta yi sanyin jiki ko jan-kafa wajen tabbatar da cewa an yi bakin kokarin ganin an lashe zabukan da ba su kammalu ba, wadanda za a maimata a wasu mazabu da rumfuna a ranar 23 Ga Maris mai zuwa a fadin Kasa nan.

Za a yi zabukan ne a jihohin Kano, Filato, Adamawa, Sokoto, Benuwai, Bauchi. Akwai zaben da INEC ta dakatar da bayyana sakamakon san a Jihar Ribas.

A dukkan wadannan jihohi, jam’iyyar PDP ce kan gaba kafin INEC ta bayyana cewa sakamakon zaben bai kammala ba. Sai a jihar Filato ce kadai APC ke gaba.

Osinbajo dai ya yi wannan furucin a lokacin da ya karbi bakuncin zaratan kungiyar kamfen na PMP/PYO da aka gayyata Fadar Shugaban Kasa domin cin abincin dare.

An gudanar da dinar ce jiya Alhamis da dare.

Osinbajo ya gode musu dangane da rawar da suka taka wajen sake zaben APC ta ci gaba da mulki a kasar nan.

Ya ce a wannan zango na biyu, tattalin arzikin Najeriya zai bunkasa sosai ta yadda Najeriya za ta zama wata kasaitacciyar kasa.

“Amma fa ina so na shaida muka cewa akwai sauran rina a kaba.

“Akwai jan-aiki a gaban mu a sauran jihohi shida da ba a kammala zabe ba. Kada mu shagala mu kwanta mu ce ai mun rigaya mun ci zabe. Tilas sai sai mun sake tashi tsaye domin ganin mun yi abin da ya rage mana mu yi.” Inji Osinbajo.

Daga nan sai kuma ya yi ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukan su a lokacin zabukan 2019.

Shi kuwa Mataimakin Shugaban Ma’aikata a Fadar Shugaban Kasa, Ade Ipaye, ya ce dama tun da Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya fadi a cikin jirgin helikwafta, aka fada masa cewa hakan na nufin APC ce za ta yi nasara.

Darakta kamfen din PMB/PYO, Buba Marwa, ya bayyana irin namijin kokarin da Osinbajon ke yi a mulkin Shugaba Muhammadu Buhari.

Ya ce wannan ne karo na farko a tarihin kasar nan da ake ganin mataimakin shugaban kasa na shiga har cikin tirmitsitsin kasuwanni ya na cakuda da talakawa.

Share.

game da Author