Shugaban Jam’iyyar APC, Uche Secondus, ya bayyana cewa babu wanda ya isa tsaida PDP zuwa kotu ta kalubalanci zaben 2019.
Haka Secondus ya bayyana haka a taro da manema labarai da ya gabatar shirya a jiya Juma’a, a Abuja.
“Tabbas za mu garzaya kotu. Ba wanda zai tsaida mu daga shekawa zuwa kotu domin mu fallasa gaskiyar ragabzar da aka yi da sunan zabe, wadda masu sa-ido na kasa da kasa da ma jama’a da dama ba su gani ba.
“Za mu fallasa asirin fallasassu a kotu, kuma na yi ammana cewa za a yi mana adalci a kotu.
“Saboda idan mu ka rika tafiya a haka, idan aka danne gaskiya mu yi shiru, a ce wai a wuce wurin, to fa mu na tara wa kanmu kwantai ne kawai na kin magance wani miki, wanda idan ya rube ya fashe a can gaba, to doyin sa zai addabe mu gaba daya.
Secondus ya kuma yi magana a kan yadda aka watsa dandazon sojoji a Kudu Maso Kudu da Kudu Maso Gabacin kasar nan a lokacin zabe.
Ya ce tura sojojin duk ya na daga cikin shirye-shiryen da aka yi domin haka PDP yin magudi.
Ya ce dalili kenan aka yi zargin karkashe mutane da sojoji suka yi, da kuma razana jama’a da aka yi suka ki fitowa su yi zabe.
Ya kara nuna cewa wadanda suka yi zabe a 2019 ba su kai kashi 36 na wadanda suka yi rajistar zabe ba, ba su kuma kai kashi 44 bisa 100 ba, yawan adadin wadanda suka yi zabe a 2015 ba.
Yayin da sojoji suka rika dankwafe jama’a a yankunan Kudu maso Kudu da Kudu Maso Gabas, a Kano, Yobe, Borno da Zamfara kuwa jam’iyya mai mulki sai ragabza a rika yi da sunan zabe.
Ya ce rahotanni sun isar musu da kuma hujjoji cewa a jihohin Barno da Zamfara ba a yi amfani da Katin Tantace Masu Zabe ba.