An yi wa matar da ta dauki bidiyon yarinya mai korafin kudin makaranta sha tara ta arziki

0

An bai wa wata mata mai suna Stephane Idolor kayutar tsabar kudi har naira 500,000 tare da mota sabuwa dal.

Idolor ita ce matar da ta dauki bidiyon karamar yarinyar nan, mai suna Success, wadda aka rika nunowa a soshiyal midiya ta na babatun an kore ta daga makaranta, saboda ba a biya mata kudin makaranta ba.

An nuno yarinyar mai shekara biyar ta na magana a fusace ta na cewa:

“Ai ba cewa aka yi ba za ni biya kudin makarantar ba. Za a biya min mana, idan an samu kudin. Amma don me za a kore ni. A jibge ni mana, maimakon a kore ni. Iyakacin ta dai idan bulalar ta gaji da duka na, shikenan. Amma mene ne kuma na kora ta.”

Wannan kalami na yarinyar ya ja hankalin jama’a da dama, inda suka rika daukar alkawarin taimaka wa yarinyar daukar nauyin karatun ta, tun daga halin da ta ke a yanzu har ta kammala jami’a.

Tuni dai yarinyar da iyayen ta su ka yi bankwana da kuncin talaucin da ya dabaibaye su, sanadiyyar jama’ar da suka maida hankali a kan su.

Ita kuma Idolor, wadda ta rika watsa bidiyon tare da yin rubutun nuna takaicin halin da yarinyar ke ciki, a halin yanzu kakar ta ta yanke saka, domin fitaccen mai barkwancin nan Mc Jollof ya shiga shafin san a Instagram ya sanar cewa Friday Osanebe, Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Delta, inda yarinyar ta ke, ya umarci a tura masa lambar asusun ajiyar banki na ta domin ya tura mata kyautar naira 500,000.00.

Sannan kuma Babban Sakataren Gwamnan Jihar Delta mai suna Hilary Ibegbulem, ita ma ta yi wa Idolor alkawarin mota sabuwa dal.

Ibegbulem ta ce ai matar da ta watsa bidoyon ita ce gwarzuwa abin yabawa sosai, domin da ba ta watsa bidiyon ba, da babu wanda zai san halin da karamar yarinyar ke ciki, har a rika tseren taimaka mata.

Shi ma mawaki Daddy Showkey Idolor, matar da ta dauki bidiyon ta na turawa kyaytar naira 100,000.

Daga cikin dimbin wadanda suka ce za su dauki nauyin yarinya mafusaciya mai suna Success, wajen karatun ta, har da Toke Makinwa, AY Makun, Wale Gates da sauran jama’a da yawa.

Share.

game da Author