An yi hauragiya, shirme da ta’addanci da sunan zabe -CDD, Kungiyar Sa-ido

0

Kungiyar Kare Dimokradiyya ta CDD, ta bayyana rashin jin dadin yadda aka tabka hauragiya, shirme da ta’addanci da sunan zabe, a jihohin da aka sake gudanar da zabukan da ba su kammalu ba.

An gudanar da zabukan ne a wasu sassan jihohin Sokoto, Kano, Filato, Bauchi da Benuwai. An jima yi na wasu daidaikun majalisar dokoki a jihohin Lagos da Imo da kuma FCT, Babban Birnin Tarayya.

CDD ta ce ta baza jami’an ta ‘yan sa ido a dukkan wuraren da aka sake zaben, kuma sun aika wa Cibiyar Tattara Bayanai na CDD da tulin bayanai marasa dadin ji da gani.

Ta ce an yi aringizon kuri’u, an yi hargitsi, an ci zarafin masu adawa, musamman a Kano, kuma an yi cinikin kuri’u sosai fiye da misali.

CDD ta ce an rika lakada wa ‘yan adawa dukan tsiya tare da saran su da adduna da takubba, da kuma yankar su da wukake.

A Jihar Sokoto, CDD ta ce an sayi kuri’a har naira 15,000.

Haka ma an kai akwatinan zabe a makare a wasu mazabu. Kamar a Karaye ta Jihar Kano da kuma Mazabar Konshishe a Jihar Benuwai.

Ba a nan CDD ta tsaya ba, ta ce an tarwatsa jama’a a rumfunan zabe tare da ingiza ‘yan-sara-suka domin su tayar da hankulan jama’a ta yadda za a yi magudin zabe.

Kungiyar sa-idon ta kara da cewa an ci zarafin jami’an zabe da kuma ‘yan jarida, musamman a Mazabar Gama, cikin Karamar Hukumar Nassarawa, Jihar Kano.

An kuma rika ganin dandazon ejan-ejan na jam’iyyar APC masu tarin yawa a kowace rumfar zabe.

CDD ta ce an yi amfani da masu dauke da muggan makamai a Nassarawa, Dala, Karaye, Gaya da wasu ka na nan hukumomin Kano da yawa, inda aka maimaita zaben.

CDD ta ce daga cikin ayyukan sa-idon da ta tura ma’aikatan ta su yi a lokacin zaben, sun hada lura da lokacin da aka fara zabe. lokacin da jami’an zabe suka isa, yadda ake tantance masu zabe, yadda ake zabe, yadda ake tattara zabe, yanayin tsaro sai kuma yanayin magoya bayan jam’iyyu.

Share.

game da Author