An yi garkuwa da matar shugaban kungiyar ‘yan jarida na jihar Nasarawa

0

Jiya Laraba ne wasu mahara su ka yi garkuwa da matar Suleiman Abubakar, tare da wasu mata uku a Karamar Hukumar Akwanga, Jihar Nasarawa.

Suleiman shi ne Shugaban Kungiyar Wakilan Kafafen Yada Labarai na Jihar Nasarawa.

An tare matar sa mai suna Yahanasu, tare da sauran matan uku wajen karfe 7 na dare, a lokacin da suke kann hanyar tafiya tsakanin titin Gudi zuwa Gareku, cikin Karamar Hukumar Akwanga.

Suleiman ya ce maharan sun tare motar da suke ciki, sannan suka bude mata wuta, a lokacin da suke komawa Lafiya daga Keffi, inda matar ta sa ta je yin rajistar shigar da sunan ta Sansanin Masu Bautar Kasa, wato NYSC.

Ya kara da cewa wutar da aka bude wa motar ta firgita direban, inda ya fada wani rami, inda nan da nan ‘yan bindigar su ka kewaye su.

Suleiman ya ce an gudu da matar sa, matar wani tsohon dan majalisar dokokin Jihar Nasarawa, da kuma wasu mata biyu da suka kama a cikin wata mota can daban.

Kakakin ‘Yan sandan Nasarawa, Samaila Usman ya ce an baza zaratan jami’an tsaro wadanda tuni suka bazama aikin tabbatar da cewa sun ceto su.

Share.

game da Author