An kara samun wani dan takarar da ya nemi kotu ta soke zaben Buhari da na Atiku

0

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar HDP, a zaben da ya gabata, Ambrose Oworu, shi da jam’iyyar sa sun maka Shugaba Muhammadu Buhari na APC da Atiku Abubakar na PDP a kotu.

Sun kalubalaci sahihancin zaben, wanda aka tsara za a gudanar a ranar 16 Ga Fabrairu, amma aka daga zuwa 23 Ga Fabrairu.

Oworu da jam’iyyar HDP su na so a soke zaben sannan kotu ta haramta nasarar da INEC ta ce Buhari ya yi a kan sauran ‘yan takara 72.

Sun kafa hujjar su da cewa doka ba ta bai wa INEC dage ranar zabe kamar yadda aka rigaya doka ta tsara ranar da za a gudanar da shi ba.

Oworu da HDP, sun yi korafin cewa a garin giriftun hayaniyar dage zabe, an cire sunan shi Oworu din da kuma sunan jam’iyyar su, HDP daga jerin masu takara.

Sun ce tunda dai sun yi rajista, kuma su na daga cikin halastattun masu takarar shugaban kasa, to INEC ta yi babban kuskure wajen buga takardun kuri’un zabe ba tare da sunan dan takarar su da kuma ita kan ta jam’iyyar ba.

Baya ga cewa su na da hujjar da za su gamsar da kutu a soke zaben, domin INEC dai babu dokar da ta ce za ta iya dafge zabe, sannan kuma sun ce INEC sun lika tsohon tambarin jam’iyyar su ta HDP, maimakon sabon wanda kowa ya sani, har da ita kan ta INEC din.

Sun ce wannan ya sa INEC ta tauye wa HDP ‘yancin shiga zabe da kuma samun kuri’u.

Sun kai kara da korafi a gaban Kotun Daukaka Karar Zabe, wadda lauyan masu marar Yusuf Ibrahim ya nemi kotun ta aika wa Buhari da APC takardar sammacen karar.

Wanda ya fara kai Buhari da Atiku kara, shi ne wani dan takarar jam’iyyar NRM a zaben Shugaban Kasa, mai suna Usman Ibrahim-Alhaji.

Shi kuma ya kai kara ne tun a ranar 6 Ga Maris, inda ya nemi a soke zaben Buhari da na Atiku, saboda dukkan su sun kashe makudan kudaden da suka wuce ka’idar da dokar zaben Najeriya ta gindaya a kashe a lokacin kamfen.

Share.

game da Author