An kama motoci biyu damfare da kuri’un zabe a Kano

0

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta yi nasarar cafke wasu motoci biyu damfare da kuri’un zabe a Kano.

An kama motocin ne a Mazabar da ke Makarantar Firamary ta Magwan, cikin Karamar Hukumar Nassarawa.

Gidan Gwamnatin Jihar Kano da kuma mahaifar Mataimakin Gamnan Jihar Kano duk a cikin Karamar Hukumar Nassarawa su ke.

Wani da aka yi abin a kan idon sa mai suna Shazali, ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa an je da motocin biyu a bayan rumfar zabe ne.

Daga nan sai wasu ma’aikatan wucin-gadi na INEC, wato NYSC su biyu suka shiga motar.

Ko da jama’a suka tambaye su abin da suke yi, sai suka ce ai su jami’an zabe ne.

Wannan tankiya ta ja hankalin jama’a, inda nan da nan aka kama su, kuma jami’an tsaro suka tafi da motocin, masu motar da kuma jami’an zaben zuwa hedikwatar ‘yan sanda ta Bompai da ke Kano.

PREMIUM TIMES HAUSA ta tabbatar da cewa rikici ya kaure a wata mazaba da ke cikin unguwar Hausawa, Kano, inda masu zabe suka ce ba su yarda a ajiye akwatin zabe a cikin daki ba.

Sun yi ta hargowar cewa tilas sai an fito da shi waje, yadda kowa zai rika jefa kuri’ar sa a fili.

Share.

game da Author