A ranar Laraba ne wasu gungun magoya bayan manyan jam’iyyu biyu da zasu fafata a zaben gwamna da na majalisar dokokin jihar Kaduna suka far wa juna a daidai suna yawon Kamfen a Unguwar Kurmin Gwari dake cikin garin Kaduna.
Kamar yadda wani mazaunin jihar ya sanar wa wakilin PREMIUM TIMES, a Kaduna, wasu ‘yan jam’iyyar adawa ce suka biyo ta unguwar da wasu ‘yan jam’iyyar suka fi yawa domin yin kamfen. Daga nan ne fa sai suka far wa tawagar masu kamfen din inda aka yi ta batakashi a tsakanin su.
Mazaunin ya ce babu wanda a aka kashe sai daian jijji wa juna rauni domin wasu ma tuni har an garzaya da su asibiti.
Kwamishinan yan sandan Kaduna Ahmed AbdulRahman ya shaida mana cewa tabbas an yi wannan arangama sai dai jami;an tsaro sun gaggauta kawo dauki inda suka tarwatsa wannan taro sannan suka tabbatar da zaman lafiya ya dawo a wannan unguwa.
Wasu sun bayyana cewa rikicin ya samo asali ne tun bayan wani arangama da ak yi wa sau masu yawan kamfen a unguwar Barnawa inda magoya bayan jam’iyyar adawa suka far musu.
A ranar Asabar ne za a gudanar da zaben gwamna da na majalisar dakokin jihohin kasar nan.