Jami’an hukumar EFCC a jihar Benuwai sun kama dan takaran gwamnan jihar na na jam’iyyar APC Emmanuel Jimeh da buhu cike makil da bandir-bandir din kudi.
Ana zargin Jimeh da fitowa da wadannan kudade domin siyan kuri’u a wajen masu zabe.
Jami’an hukumar zabe EFCC ne suka ritsa wannan dantakara dauke da wadannan kudade a mazabar Bank, dake garin Makurdi, Jihar Benuwai.