Babbar kotun dake jihar Filato ta gurfanar da Gundumi Saya mai shekaru 42 da ta kama da laifin kashe buduwarsa wanda matan aure ce mai suna Hajara Markus.
Saya na auren mata uku da ‘ya’ya 14 dake zama a Zango Dinya a karamar hukumar Bassa sannan ya aikata wannan ta’asa ne ranar 21 ga watan Nuwamba 2018.
Rundunar ‘yan sandan jihar ta bayyana cewa bayan kashe Hajara da Saya ya yi ya jefar da gawar ta ne a bakin titi abun sa.
A bayanan da ya yi a kotu Saya ya ce Hajara tsohuwar budurwar sa ce tun suna matasa sannan sun ci gaba da holewarsu tare duk da auren da suka yi.
” Na kan kira Hajara ta waya sai mu hadu a wani wuri mu ci gaba da abinda muka saba yi.
Ya ce a wata rana ya karbi aron dakin abokinsa mai suna Ojuku domin shi da Hajara su kwana tare. Da Hajara ta zo sai matar Ojuku ta aiko dan yaro da garin kwaki da kuli wanda Hajara ta karba ta sha sannan muka kwanta.
A Ciki dare da na tashi domin mu ci gaba da harka kawai sai na taba ta naji shiru, da na rigingina ta sai naga ay a muce take. Ashe ta riga ta mutu.
Saya ya kara da cewa daga nan ne ya kira Ojuku domin su san yadda za suyi.
” Da Ojuku ya zo sai ya bani shawaran mu jefar da gawar Hajara a bakin titi cewa hakan zai sa abin ya zo da sauki.
Saya yace bayan kwanaki shida wata rana sai ya ji hayaniya a kofar gidan sa da ya leko ta tagar dakin sa sai ya hango dandazon ‘yan sanda sun yi cincirundo a waje.
” A haka dai sai na samu na sulale na koma daji ina kwana har na tsawon kwanaki uku. Bayan na ji wai jami’an tsaro sun kama wana sai kawai na fito na mika kai na.
Shiko mijin Hajara Markus Jagaba mai shekaru 44 ya bayyana wa kotu cewa a wannan rana Hajara ta shaida masa cewa zata yi ‘yar gajeruwar tafiya ne zuwa garin Bauchi domin halartar bukin aure.
” Na yi ta kokarin kiran ta a waya amma bai shiga ba. Da na kira ‘Yan uwanta a can Bauchin sai suka ce ay bata zo Bauchi ba sannan kuma ma bukin an gama shi tuni.
Markus ya ce bayan ‘yan kwanaki da kai karan bacewar Hajara ofishin ‘yan sanda ne ‘yan sanda suka nemi shi yazo domin tabbatar da gawar Hajara.
” Ko kadan bani da masaniyar cewa Hajara matata na da wani saurayi a rayuwarta sannan karya ta yi mun domin ta je ta sami shi.
Alkakin kotun Daniel Longji ya daga shari’ar zuwa ranar daya ga watan Afrilu.
Discussion about this post