Allah Yace Ku Roke Shi, Zaya Amsa Maku, Daga Imam Murtadha Gusau
Lahadi, Jumadal-Thani 25, 1440 AH (March 3, 2019)
Bismillahir Rahmanir Rahim
Ya ku bayin Allah! Ku sani cewa dukkanin halitta mabukata ne a wurin Ubangijin su, wurin jawo masu amfani da biya masu kyawawan bukatun su, da kuma yaye masu cututtuka da kare su daga dukkanin sharri, domin gyaruwar lahirar su/addinin su da duniyar su. Kuma muna sane da cewa, kamalar mutum tana tattare ne da tabbatar da bautar sa ga Allah mai girma da daukaka. Kuma a duk lokacin da bawa ya kara tabbatar da bautar sa ga Allah sai kamalar sa ta karu, kuma darajar sa ta daukaka. Kuma Allah mai girma da daukaka yana jarraba bayin sa da wasu abubuwa masu bijirowa da sukan tura su zuwa ga kofar sa, domin su nemi agajjin sa. Kuma bukatuwa zuwa ga Allah, ita ce hakikanin wadatuwar sa. Kuma kaunar bauta da babbar manufar ta, da kuma kaskantar da kai ga Allah mai tsarkin mulki shine daukakar da ba za’a iya gasa da ita ba. Kuma Addu’a ita ce alamar bauta, Allah yana son bayin sa su roke shi a cikin dukkannin bukatun su. Domin yazo cikin littafin Sahihu Muslim daga Hadisin Abi Zar, Allah Ya kara yarda a gare shi, Allah Madaukakin Sarki Ya ce:
“Ya ku bayi na! Dukkanin ku batattu ne sai fa wanda na shiryar da shi, to ku nemi shiriya ta, zan shiryar da ku. Ya ku bayi na, dukkanin ku mayunwata ne, sai fa wanda na ciyar da shi, to ku nemi ciyarwa ta, zan ciyar da ku. Ya ku bayi na, dukkanin ku tsirara kuke, sai fa wanda na tufatar da shi, to ku nemi tufatarwa ta zan tufatar da ku. Ya ku bayi na, hakika kuna yin kuskure dare da rana, ni kuma ina gafarta zunubai baki daya, ku nemi gafara ta zan gafarta maku.”
Ya ku bayin Allah! Ku sani cewa, Allah (SWT) ya hore hanyoyin samun rabo, kuma ya huwace hanyoyin tabewa. Kuma ya jera abubuwa masu faruwa a bisa dalilan faruwar su, kuma ya halicci sakamakon da zasu haifar. Kuma babu wani abu da yake hukunta kansa da nufin sa. Da yaso da ya samar da abu ba tare da sababi ba. Allah Ta’ala Yace:
“Shi mai aikatawa ne ga abin da yayi nufi.”
Kuma Allah Madaukakin Sarki ya ce:
“Lalle halitta da umarni nasa ne. Albarkatun Allah sun yawaita. Ubangijin talikai.”
Don haka, Addu’a dalili ne babba na rabauta da alkhairai da albarkoki. Kuma dalili ne na yaye ko wane irin bakin ciki, damuwa, sharri da bala’i. Kuma babbar hanya ce ta samun biyan bukatu a wurin Allah, Madaukaki.
Imamu Tirmizi ya ruwaito daga Ibn Umar (RA) yace:
“Addu’a tana amfani ga abin da ya sauka, da ma wanda bai sauka ba.”
Addu’a tana daga cikin kaddara, kuma sababi ce daga cikin sabubba masu amfani, masu janyo alkhairi, su kuma yaye dukkanin sharri. Hakika, Allah yayi umarni da yin Addu’a a cikin ayoyi masu tarin yawa, misali, yace:
“Kuma Ubangijin ka yace, ku roke ni, zan amsa maku. Hakika wadanda suke yin girman kai ga barin bauta mani (barin roko na) zasu shiga wutar Jahannama suna kaskantattu.”
Ya ku bayin Allah! Ku sani cewa hakika yin Addu’a shine: tsananta kwadayin bawa ga Allah Ta’ala wajen neman biyan bukatun duniya da na lahira, da yaye bakin ciki da damuwa, da kade sharri, da bala’i na duniya da lahira.
Da Addu’a ne bautar Ubangijin talikai take tabbata, domin ta kunshi ratayuwar zuciya ga Allah Ta’ala da Ikhlasi gare shi, da rashin waiwayen wani ba shi ba.
Addu’a ta kunshi sakankancewa da cewa Allah mai cikakken iko ne, mai biyan bukatun bayin sa ne, babu wani abu da zai gajiyar da shi ko ya gagare shi, babu wani abu da zai buya a gare shi, mai rahama mai jinkai. Allah, Rayayye ne, mai isa da zatin sa, ma’abocin alkhairi har abada, ba’a iyakan ce baiwar sa da alkhairin sa. Taskokin albarkatun sa basa karewa.
Addu’a ta kunshi bukatuwar bawa da tsananin matsuwarsa zuwa ga Ubangijin sa, hakika, wadannan abubuwa sune hakikanin ma’anar Ibada.
Ya ku bayin Allah! Hakika dimbin nassoshi na Hadisan Annabi (SAW) sun zo game da falalar Addu’a. Daga cikin su akwai abinda Abu Dawud da Tirmizi suka ruwaito daga Nu’man Bin Bashir, Allah ya kara yarda a gare su daga Annabi (SAW) ya ce:
“Addu’a ita ce Ibada.” [Imamu Tirmizi yace: Hadisi ne kyakkyawa, ingantacce]
Kuma an karbo daga Abu Hurairah Allah ya kara yarda a gare shi yace, daga Annabi (SAW) yace:
“Babu wani abu da yafi girma a wuri Allah kamar Addu’a.” [Imamu Ahmad da Tirmizi da Ibn Majah da Ibn Hibbana ne suka rawaito]
Hakanan an ruwaito daga Abu Hurairah (RA) yace, Manzon Allah (SAW) yace:
“Hakika Allah mai girma da buwaya yana cewa: “Ni ina tare da zaton bawa na gare ni, kuma ni ina tare da shi (da sani na) idan ya ambace ni.” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi, kuma lafazin sa ne. Haka nan Tirmizi da Nasa’i da Ibn Majah duk sun rawaito shi]
An karbo daga Ubadah Dan Samit (RA) cewa, Manzon Allah (SAW) yace:
“Babu wani Musulmi a bayan kasa da za ya roki Allah da wata Addu’a face ya biya masa ita; ko dai ya kade masa wani mummunan abu a madadin ta, matukar ba ya roki wani abin laifi ba ko yanke zumunci…” Sai wani mutum daga cikin mutane yace: “Ashe zamu yawaita ke nan.” Sai yace: “Allah Shine mafi yawaita wa.” [Imamu Tirmizi ne ya rawaito kuma ya inganta shi]
Ya ku bayi Allah! Ku sani cewa ba’a rokon kowa sai Allah, ba wani Mala’ika makusanci ga Allah, ko wani Annabi mursali, ko wani waliyyi nagartacce. Kuma duk wanda ya kira wani abun halitta ba Allah ba, Annabi ne ko Mala’ika, ko waliyyi, ko aljan, ko kabari, ko makamancin sa, to hakika yayi shirka da Allah Ta’ala, cikin Ibadar sa, kuma shirka wadda zata fitar dashi daga cikin Musulunci (wato ridda). Allah Ta’ala yace:
“Kuma hakika Masallatai na Allah ne, don haka kada ku kira wani tare da Allah.”
Kuma Allah Madaukakin Sarki yace:
“Kuma wanda ya kira yi wanin Ubangiji tare da Allah wanda ba shi da wani dalili (ga bauta masa), lallai to wannan hisabin sa yana wurin ubangijin sa, kuma lallai kafirai ba zasu rabauta ba.”
Kuma Allah Ta’ala yace:
“Kada ka kirawo wani ba Allah ba, wanda ba za ya amfane ka ba, kuma ba za ya cutar da kai ba, idan kuwa ka aikata haka, to lallai kai kana cikin azzalumai.”
Kuma yace:
“Kuma idan Allah ya jarrabe ka da wata cuta to babu mai iya yaye maka ita face shi, idan kuma ya nufe ka da alkhairi to babu mai mayar da falalar sa, yana samar wa wanda yaso daga bayin sa da shi, kuma shine mai gafara mai Jinkai.”
Kuma Allah Ta’ala yace:
“Kuma ranar da za ya tashe su gaba daya sannan yace da Mala’ikun sa, shin wadannan ku ne suka kasance suna bautawa? Sai suce tsarki ya tabbata a gare ka, kai ne majibincin mu, ba su ba. Kadai sun kasance suna bautawa aljannu ne mafi yawancin su masu ba da gaskiya ne da su.”
Ya ku Musulmi! Hakika Addu’a tana da lokuta na musamman, kuma wadanda aka fi kaunar amsa ta a cikin su, wadanda sune kamar haka:
1. Addu’a a cikin Sujjadah.
Daga Abu Huraira Allah ya yarda da shi, daga Annabi (SAW) yace:
“Lokacin da bawa yafi kusa da Ubangijin sa, shine lokacin da yake cikin Sujjadah. Don haka, ku yawaita Addu’a a cikin ta.” [Imamu Muslim ne ya ruwaito shi]
Kuma an karbo daga Ibn Abbas (RA), yace: MAnzon Allah (SAW) yace:
“Lallai hakika ni an hana ni in karanta Al-kur’ani a cikin ruku’u ko Sujjadah. Amma ruku’u to ku girmama Ubanjigi a cikin sa. Ita kuma Sujjadah, kuyi matukar kokari wajen yin Addu’a a cikin ta, lallai ya dace a amsa muku.” [Muslim ne ya rawaito shi]
2. Tsakanin kiran Sallah da Ikama.
Domin an ruwaito daga Anas (RA) yace: Manzon Allah (SAW) yace:
“Ba a mayar da Addu’a a tsakanin kiran Sallah da Ikama.” [Imamu Tirmizi ne ya fitar da shi, kuma yace, Hadisi ne kyakkyawa, ingantacce]
3. Idan sulusin dare na karshe ya rage.
Domin yazo a cikin Sahihul Bukhari, Manzon Allah, tsira da aminci su tabbata a gare shi yace:
“Ubangijin mu (Allah) ya kan sauka (irin saukar da ta dace da shi), ko wane dare zuwa saman duniya yayin da sulusin dare na karshe ya rage, sai yace: “Wanene za ya kira ni in amsa masa? Wane ne za ya nemi gafara ta in gafarta masa?”
4. Karshen sa’a (lokaci) bayan Sallar La’asar ranar Juma’ah.
An ruwaito daga Abi Huraira (RA) cewa Manzon Allah (SAW) ya ambaci ranar Juma’ah sai yace:
“A cikin ta (Juma’ah) akwai wata sa’a (lokaci), babu wani bawa Musulmi da zai dace da ita a tsaye yana Sallah, yana rokon Allah wani abu face ya bashi. Yayi nuni da hannun sa yana karanta ta.” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi]
Ma’abota ilimi suna da mazhabobi da dama wajen tantance wannan sa’ar (lokacin) na ranar Juma’ah. Amma mafi inganci shine cewa, karshen sa’a bayan La’asar, kamar yadda yake a cikin Hadisin Abi Dawud da wanin sa, Annabi (SAW) ya ce:
“Ranar Juma’ah sa’a sha biyu ce, ba za’a samu wani Musulmi yana rokon Allah wani abu a cikin ta ba face ya bashi. Ku neme ta a sa’a ta karshe bayan Sallar La’asar.”
5. Daren Lailatul Qadari.
6. Ranar Arafah a aikin Hajji.
7. Wurin Hajarul Aswad a Makkah.
8. Yayin saukar ruwan sama.
9. Bayan Sallolin farillah.
10. Lokacin shan ruwa (buda-baki) yayin azumi.
11. Lokacin shan ruwan Zamzam.
12. Yin tawassuli da wani aikin alkhairi, kamar sadaka da sauransu.
Duk wadannan lokuttan amsa Addu’a ne, sai muyi kokari, tare da bada himmah wurin yawaita Addu’o’i a cikin su. Allah yasa mu dace, ya karbi dukkanin addu’o’in mu, amin.
Ya ku bayin Allah! Kuyi kokari ku ganimanci falalar Ubangijin ku, ku fake zuwa gare shi cikin dukkanin al’amurran ku. Ku daukaka tafukan ku zuwa sama da kaskan da kai zuwa ga re shi, ko a amsa Addu’o’in ku, sannan kuma ku rabauta da yardar Ubangijin ku!
Kar kuyi kokwanton amsa Addu’o’in ku!
Yana da kyau mai yin Addu’a ya kaskantar da kansa ga Ubangiji, sannan ya cire kokwanton amsa Addu’ar a zuciyar sa.
An karbo Hadisi daga Buraidata (RA) yace: Manzon Allah (SAW) yaji wani mutum yana cewa:
“Allahummah inni as’aluka bi anni ash-hadu annaKa antallahu Laa ilaaha illa anta, al-ahadus samadu, allazi lam yalid wa lam yulad wa lam yakun lahu kufwan ahad.”
Sai Manzon Allah (SAW) yace:
“Lallai kayi roƙo da sunan da Idan aka yi roƙo da shi ana bayarwa, kuma idan aka yi Addu’a da shi ana amsawa.” [Mutane hudu suka ruwaito shi, Ibn Hibban ya inganta shi]
Wannan Hadisin na nuna mana kenan ana saurin amsa Addu’ar wanda yayi amfani da wadannan sunayen kenan.
Saboda haka ‘yan uwa, Idan za kuyi Addu’a, sai ku fara ambaton wadancan sunayen, kuyi ma Allah kirari, ku yabe shi, sannan sai Addu’ar ta biyo baya.
Ina neman gafarar Allah Madaukaki, Mai girma, ga kaina da ku baki daya, da kuma sauran Musulmi daga ko wane zunubi. Lallai shi Mai yawan gafara me, Mai yawan jinkai ga bayin sa.
Wassalam Alaikum,
Dan uwanku:
Imam Murtadha Muhammad Gusau, daga Okene, Jahar Kogi, Nigeria. Za’a iya samun shi a: gusaumurtada@gmail.com ko kuma 08038289761.