Alkalin Kotun Koli ya zama Sarkin Lafiya

0

An nada Mai Shari’a Sidi Bage na Kotun Kotun Koli a matsayin sabon Sarkin Lafiya.

An nada Bage ne a matsayin sarki na 17, biyo bayan rasuwar Sarki Mustapha Agwai I, wanda ya rasu ranar 20 Ga Janiru.

Mr Agwai died on January 10.

Kwamishinan Kananan Hukumomin da Masarautu, Haruna Osegbe ne ya bayar da wannan sanarwa ta nada Sarkin Lafiya, a jiya Talata, bayan da Majalisar Sarakunan Jihar ta gudanar da taron ta.

Osegbe y ace Majalisar Zababbun da ke Nada Sarki ce ta zabi sabon sarkin, shi kuma Gwamna Umaru Al-makura ya rattaba hannun amincewar sa.

Ya ce an zabi sabon sarkin a bisa doka da ka’idar da aka shimfida a cikin 1986, wato Doka ta 12, Sashe na 31, wadda ta ce a rika yin tsarin karba-karba wajen nada sarautar Sarkin Laiya a tsakanin Gidan Sarauta Biyu da ke Masarautar.

Bage da Musa Mustapaha Agwai, dan sarkin da ya rasu ne suka yi takarar neman sarautar.

Sai dai kuma masu nada sarki hudu daga cikin su biyar, sun zabi Bage, sai daya ne kadai ya zabi Musa, dan sarkin da ya rasu.

An haifi Bage ranar 22 Ga Yuni, 1956.

Baya ga Bage kuma, Gwamna Al-makura ya amince da nadin Isa Abubakar a matsayin sabon Sarkin Awe, bayan rasuwar tsohon sarkin.

An zabi Isa Abubakar ba tare da wata ja-in-ja ba a tsakanin mutane hudu masu hakkin nada sarki a kasar Awe.

An kuma zabi Umar Dodo a matsayin sabon ‘Osu Kadarko’, wato Sarkin Keana.

Dodo a yanzu ya zama Sarkin Keana, bayan rasuwar Sarki Fabian Orogu a ranar 12 Ga Janairu, 2018.

Share.

game da Author