AIKIN GAMA: Dalilai 19 Da Ka Iya Sa Abba Gida-gida Gamawa Da Ganduje A Kotu, Daga Ashafa Murnai

0

Na kalli wani bidiyo da aka rika watsawa a soshiyar midiya, yau Asabar da rana. A gaskiya na ji tausayin Gwamnan Jihar Kano, irin yadda na ga dandazon matasa na bin kwanba din motocin da su ka yi jerin-gwaron rakiyar gwamnan, har da motar da shi kan sa ya ke ciki.

Matasa da kananan yara, har ma da wadanda ba su wuce shekara goma ba, sun rika bin motar Ganduje su na surfa zagi, sheka ruwan ashariya da kuma aibata shi da munanan kalaman da ke nuna cewa ba zaben gaskiya-da-gaskiya ya ci ba, fashin kuri’u da murdiya ya yi.

Amma kuma ban ji tausayin Ganduje ba, domin idan har Kotun Daukaka Kara da kuma Kotun Koli suka tabbatar da cewa fashin kuri’un ya yi, to ban ga dalilin da zan ji tausayin sa ba.

Bari na yi shimfidar rubutu na da wani baitin wakar Dankwaro, wadda ya yi wa Marigayi Shugaban Kasa Shehu Shagari, bayan ya yi nasarar zabe a lokacin Jamhuriya ta Biyu.

Baitin ne ya fado min a rai, lokacin da na ke kallon bidiyon da ake bin Ganduje a cikin motar sa ana keta masa mutunci.

“Ni Alhaji Musa na ci dariya,
Na koma na yi mamaki,
Dannan kuma na ji tausan maza,
Siyasar ga wadda ta hurce,
Ga wasu sun ci zaben kwarai,
Ga wasu kau ba su ci zaben kwarai ba,
Ai ga wasu sun ci kubeji,
Wasu kau kunku sun ka ci,
Dan ba su da dadin rai daji,
Kuma ba su da dadin rai binni,
Shi yaz zama hasken balbela,
Balbela idan tat taso,
Sai ka ga jikin ta zah hwari,
Amma cikin naman nan na ta zab baki.”

Irin yadda ake ta yayata cewa Ganduje bai ci zaben kwarai ba, to idan aka yi la’akari da cewa kotu ce za ta raba wannan gardama da kokawa, kenan wannan zabe Ganduje ya cin kubeji.

Sannan kuma irin yadda na dan Ganduje na yawan sanya fararen kaya, idan su ya saka a ranar yau Juma’a da matasa suka bi shi su na eho da sowar muzanta shi, duk da cewa tufar sa fara ce, to a zuciyar sa akwai bacin ran abin da aka yi masa. Sai dai a ce ta-ciki-na-ciki kawai.

Na yi hasashen yadda za ta kaya a Kotun Daukaka Kararrakin zabe, yadda na ke ganin cewa Ganduje ba zai sha da dadi ba.

Babu ko tantama Ganduje ya ga abin da ya faru da APC da aka je kotu a Jihar Ribas, a Jihar Zamfara da Jihar Osun.

Idan kuwa yayi tagumi ya tuna da sakamakon hukuncin kotu a kan wadannan jihohi, watakila a lokacin zai tuna da karin maganar Bahaushe da ya ke cewa, “Abin da ya ci garin Doma, ba zai bar garin Awai ba!

KO DAI AIKIN GAMA ZAI GAMA DA GANDUJE A KOTU NE?

1 – An tabbatar da hargitsa kuri’un Gama da aka yi a zaben farko na ranar 9 Ga Maris, wanda aka kama Mataimakin Gwamna, Nasiru Gawuna, Kwamishina Murtala Sule Garo da Shugaban Karamar Hukuma.

2 – An tabbatar da an kekketa kuri’u da dama a wurin.

3 – A zabe na biyu da aka maimaita, an tabbatar da tafka magudi da jam’iyya mai mulki a Kano, APC ta yi a wurare da dama.

3 – An tabbatar da tada hankulan jama’a, cin zarafin ‘yan jam’iyyar adawa, hana wasu da dama yin zabe. Wasu kuma kafin su je har an dangwale kuri’un na su.

4 – An tabbatar da ’yan-ta-kife sun sari mutane da dama, aka jikkata masu tarin yawa.

5 – An tabbatar da yin hatsaniya, a wuraren da zugar ‘yan-ta-kife dauke da muggan makamai suka rika fatattakar masu zabe.

5 – An tabbatar da cin zarafin masu sa-ido kan zabe.

6 – An tabbatar da cin zarafin ‘yan jarida ba daya ba.

7 – An tabbatar da sakacin jami’an tsaro a wasu wurare.

8 – Bayanai da dama sun ki gamsar da jama’a yadda PDP da dan takarar ta Abba Yusuf ba su ci kuri’un kirki a zaben da aka maimaita ba.

9 – Bayanai sun kasa gamsar da jama’a da yawa, yadda Ganduje da APC suka samu tulin kuri’un da suka wuce misali, har a mazabun da PDP ke da rinjaye da kuma inda rahotanni suka nuna an hana masu adawa fitowa su yi zabe.

10 – Rahotanni sun nuna akwai inda maza suka shiga layi da katin zaben mata suka rika dangwala kuri’a.

11 – Akwai bidiyo da dama wadanda suka rika nuna yadda ‘yan-takifen APC suka rika tayar da hargitsi da yamutsi da rincimi a wuraren zabe. Kuma sun a dauke da muggan makamai.

12 – Yadda Maitaimakin Sufeto Janar na ’Yan Sanda mai lura da yadda aka gudanar da zaben da aka maimaita a ranar 23 Ga Maris, ya ce an yi zabe lami lafiya.

13 – Wannan abin dubawa ne da iron basira, musamman idan alkalai suka gamsu da cewa an tafka yamutsin hargitsa zabe da kuma hana ‘yan adawa yin zaben da sauran hauragiyar da ta faru a ranar.

Kungiyar Tarayya Turai ta gamsu da bayanan da masu sa-ido suka gabatar mata cewa an yi haurgiya a zaben.

Kungiyoyin sa-ido na cikin gida na sauran na kasashen ketare sun ce an yi hauragiya, an yi amfani da makaman da aka ji wa masu adawa raunuka.

Amnesty International ma ta ce a binciki abin da ya faru ranar zaben.
’Yan jaridu da dama sun bada labarin wainar da aka toya. Wadanda aka ci wa zarafi kuma sun bayyana abin da ya faru da su.

Babbar hujja kuma ita ce kasassabar da Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Kano, Abdullahi Abbas ya yi, inda aka nuno shi a wani bidiyo kafin zabe ya na rantsuwa cewa ko PDP ta ci zabe ba za su ba ta ba. Su ke da gwamnati, su ke da sojoji, su ke da ’yan sanda, kuma su ke da SSS.

Duk a cikin bidiyon an nuno shi ya na zuga wasu gungun matasa kana bin da ya ke so su yi a ranar zabe. Shin wadanne hujjoji kotu za ta kara nema, fiye da wadannan?

Share.

game da Author