Hukumar hana yaduwar cututtuka ta kasa (NCDC) ta bayyana cewa zazzabin lassa na ta kara yaduwa a kasar nan inda a watan Janairu kawai mutane 42 suka rasa rayukan su a dalilin kamuwa da cutar.
NCDC ta bayyana cewa daga ranar daya zuwa 27 ga watan Janairu hukumar ta gwada jinin mutane 538 inda sakamakon gwajin ya nuna cewa mutane 213 na dauke da cutar sannan daga ciki mutane 42 sun rasa rayukan su.
Hukumar ta gano haka ne daga jihohi 16 da suka hada da Edo, Ondo, Bauchi, Nasarawa, Ebonyi, Plateau, Taraba, Abuja, Adamawa, Gombe, Kaduna, Kwara, Benue, Rivers Kogi da Enugu.
Rahotan ya nuna cewa ma’aikatan kiwon lafiya hudu sun kamu da cutar duk a watan Janairu.
NCDC ta ce a yanzu haka mutane 102 na samun kula a asibitocin da aka bude a kasar domin kula da masu dauke da cutar.
A karshe jami’in kungiyar kula da kiwon lafiya ta duniya (WHO) Peter Clement ya ce ganin yadda cutar ke yaduwa a Najeriya kusan duk shekara ya sa kungiyar za ta kara zage damtse wajen ganin ta tallafa wa kasar domin dakile yaduwar cutar.
Da hanyoyin guje wa kamuwa da cutar
1. Da zaran mutum ya kamu da zazzabi a tuntubi likita domin tabbatar da cutar da mutum ke dauke da shi.
2. Duk ma’aikacin kiwon lafiya da zai duba mara lafiya a asibiti ya tabbata yana sanye da safar hannu sannnan ya kuma tabbata ya wanke hannayen sa da kyau bayan ya gama duba mara lafiya.
3. Ma’aikatan kiwon lafiya su tabbatar sun nemi magani da zarar alluran da suka yi amfani da shi a jikin wanda ke dauke da cutar ya soke su.
4. A tabbata an tsaftace muhalli da kuma adana kayan abinci neasa da fitsari da kuma kashin beraye.
5. Ba a iya kamuwa da cutar zazzabin Lassa idan an taba wanda ke dauke da cutar amma za a iya kamuwa da shi idan yawu, jini ko kuma zufan wanda ke dauke da cutar ya taba wanda ba ya da shi.