Gwamnan Jihar Barno Kashim Shettima ya yi barazanar cewa kwanan nan sai sake komawa garin Gamboru Ngala, duk kuwa da harin kwanton-bauna da Boko Haram suka yi masa cikin makon da ya gabata.
Shettima ya bayyana haka ne a jiya Talata, lokacin da ya ke ganawa da manema labarai, Jim kadan bayan taron sirri da ya yi shi da wasu gwamnoni a Fadar Shugaba Buhari.
Ya ce haka zikau din sa zai tafi a cikin game-garin mota, ba zai shiga mota mai silken hana harsashi shiga ba.
Idan ba a manta ba, PREMIUM TIMES ta kawo rahoton yadda Boko Haram su ka yi wa tawagar kamfen na zaben gwamna kwanton-bauna tare da bude musu wuta.
Soja daya ya rasa ran sa, kuma wasu sun mutu a harin. Duk da haka dai Shettima ya ce shi sai ya koma harin, ko da kuwa zai sadaukar da ran sa ne kacokan.
Ya ce ai duk wanda ke ahugabanci to ya san akwai nauyin jama’a a kan sa.
“Don haka, matsawar ina shugaba kuma a akwai inda ba na iya zuwa wurin da jama’a ta su ke, ai za su rika yi min kallon shin wane irin gwamna ne kuma su ke da shi?
Shettima ya ce ahugabanci ba na matsoraci ba ne. Duk da irin hare-haren da Boko Haram ke yawan kaiwa, Shettima ya ce an samu ci gaba a karkashin mulkin Buhari.