Zamu saka wa Uba Sani da ambaliyar Kuri’u a zaben 16 ga wata – Ibrahim Rigasa

0

Fitaccen dan siyasa kuma wanda ke kan gaba wajen tallata jam’iyyar APC, shugaba Muhammadu Buhari da gwamna Nasir El-Rufai sannan dan takarar kujerar Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Mal Uba Sani ya sami ya sami yabo na arziki daga mutanen yankin Kaduna ta tsakiya fa ya hada kananan hukumomin Kaduna Ta Arewa, Kaduna Ta Kudu, Birnin Gwari, Kajuru, Chikum da Giwa.

A jihar Kaduna, a karon farko an sami dan siyasar da ya rungumi kowa sannan ya warware Kullin nan da ya cukuykuye ‘yan siyasan jihar da aka dade ana fama da shi musamman wajen yin adalci ga ‘yan siyasa.

Baya ga shimfida yanayi na siyasa da ta dace da mutanen jihar, ya bude kunnuwar sa bibbiyu domin sauraren koke-koken su da share musu hawaye.

Baya ga haka ya maida hankali wajen ganin matasa da musamman mata sun samu tallafi yadda ya kamata da kuma shirye hanyoyi na musamman domin isar da sakon su ga majalisar kasa domin samun abin dogaro ga.

Wasu da dama daga cikin mutanen yankin Kaduna ta Tsakiya suna cewa lallai sun yi sa’a da takarar Mal Uba dan takarar sanata na shiyyar.

” Idan da a ce za a bamu dama da mu ko tun a yanzu ma a canja. Uba ya yi mana halasci a Kaduna ta Tsakiya. Abinda za mu yi masa shine mu saka masa da buhu-buhun kuri’u a ranar 16 ga wata.

” Sanatan da ke kai yayi mana alkawurra da dama amma kuma duk ashe tatsuniya ce. Babu abinda bai ce zai yi sai gashi abun ya zama hira ba mu ga komai ba.

” Malam Uba ya taka rawar gani a musamman siyasar Kaduna. Ya rufe idanun sa da kunnuwar sa daga sauraren labaran kanzon kurege. Ya rungumi jama’a. Yana yi wa kowa hidima ta arziki domin cigaban al’umma” Inji Ibrahim Mohammed, Mazaunin Garin Rigasa.

Share.

game da Author