ZAMFARA: Mahara sun kashe kanwar Sanata Kabiru Marafa sun yi garkuwa da mijinta

0

Sanatan dake wakiltan Zamfara ta tsakiya, Kabiru Marafa ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa masu garkuwa da mutane sun kashe kanwar sa Ade Marafa sannan sun yi garkuwa da mijinta.

Marafa ya bayyana cewa maharan sun kashe Ade da misalin karfe 3 na dare ne sannan suka far wa wasu kauyukan dake kusa da kauyen Ruwan Bore.

Sanata Marafa ya ce gidan su ne kawai suka far ma inda suka kashe kanwar sa amma sauran gidajen kauyukan duk banka musu wuta suka yi.

Idan ba a manta ba Jihar Zamfara ta yi kaurin suna wajen ayyukan ta’addanci. Ya kan yi wuya a yi kwanaki biyu ba tare da an kai hari wani kauye ba ko kuma an kashe wani ko kuma an yi garkuwa da wani jihar.

Mutane sun gudu daga kauyukan su da dama inda duk sun dawo garin Gusau da wasu manyan garuruwan jihar.

Share.

game da Author