Duk da alwashin da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta sha bayarwa cewa Na’urar Tantance wanda ya yi rajista, wato Smart Card Reader ba za ta bayar da matsala ba, rahotanni sun tabbatar da cewa a wasu yankuna da dama na kasar nan na’urorin ba su yi moriya ko amfana komai a wurin zaben ba.
Wannan ya kawo haushi, fushi da harzuka masu zabe da dama. Sannan kuma sun yi matukar kawo jan-kafa da latti a wajen jefa kuri’a.
An shigo da tsarin amfani da na’urar tantance mai zabe, a cikin 2015. Da shi ne ake tantance katin rajista na dindindin da kowa ya yanka.
INEC da kan ta ta rika kwarzanta na’urar cewa it ace kadai za ta iya magance magudin zabe a kasar nan. Kuma idan aka shigo da tsarin yin amfani da ita, to babu wanda zai yi zabe sai wanda na’urar ta tantance kadai.
An kuma saisaita na’urorin yadda kowace ga rumfar zaben da za ta iya aiki kawai, ko an kai ta wata mazaba, ba za a iya amfani da ita can ba, ballantana har a yi magudi ko harkalla da ita.
YADDA NA’URA TA HAIFAR DA JINKIRI A JIHOHI DA DAMA
Jihohi da dama da wakilan PREMIUM TIMES suka zagaya, sun gano cewa jami’an INEC da ma’aikatan INEC na wucin-gadi, musamman ‘yan bautar kasa, NYSC, sun rika shan gaganiyar amfani da na’urar a fadin kasar nan.
A rumfar zabe ta 006 da ke Firamaren Kofar Kudu a Gezawa cikin jihar Kano, ba a fara zabe ba sai karfe 11 na safe, saboda ‘card readers’ sun kawo matsaloli.
Haka abin ya ke a rumfar 033 cikin Karamar Hukumar Fagge ta jihar Kano, su ma ba a fara zabe ba, sai bayan 11:30 na safe, saboda wannan na’urar tantance kati da mai katin rajista din uk sun ki aiki.
A Shiyyar Ajiya, cikin Karamar Hukumar Tambuwal, cikin jihar Sokoto, can ma ba a fara zabe ba sai bayan 11:21, saboda matsalar na’ura.
An samu irin wannan matsala a jihar Enugu, jihar Kogi da wasu jihohi da dama.
Wasu jami’an zabe sun rika shiga dawurwura da tunanin shin su kyale jama’a su jefa kuri’a ne kawai, ko kuwa su ci gaba da bata lokacin jiran gawon-shanu har sai lokacin da ‘card reader’ ta fara aiki tukunna?
Wasu na ganin cewa tunda akwai sunayen masu zaben, kuma ga katin su a hannu, to a bar su kawai su yi zabe, ko da babu na’urar tantancewa mai tantance su.
A wata rumfar zabe da ke unguwar Achara a Enugu, har karfe 11:55 ana ta gaganiyar yadda za a yi na’ura ta yi aiki.
Dalili kenan Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce shi dai bai gamsu da aikin na’urar tantance katin kuri’a ta yi a zaben na yau ba.
Bello ya yi zabe ne a mazabar Agasa, shi da matar sa.
Gwamnan ya rika shan wahalar fama da card reader. Har ma akwai lokacin da ya koma cikin mota ya na zauna ya huta da na’ura ta ki tantance shi.
Shi ma dan takarar shugaban kasa, Kingsley Moghalu, ya ce an sha wahalar tantancewa da na’ura a mazabar sa ta Nnewi ta Arewa, Mazaba ta 2.
Ya shaida wa Gidan Talbijin na Channels cewa a mazabar sa na’ura ta guma wa masu zabe bakin ciki.
“Na fita tun karfe 8 na safe domin na yi zabe, amma na je na samu ana ta gaganiya da na’urorin tantance katin mai zabe. Tilas na koma gida, sai 12 na rana na sake fita.” Inji Mugalu.