Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta bayyana cewa ta shigo da wasu sabbin dabarun cafke masu sayen kuri’u a ranar zabe.
Daraktan Wayar Da Kai Da Yada Labarai, Festus Okoye ne ya bayyana haka, jiya Lahadi a Abuja.
Okoye ya ce INEC ta damu da yadda wasu ‘yan siyasa suka rika sayen kuri’u a wasu zabuka a cikin 2018. Don haka ne suka bijiro da sabbin dabarun kama su.
Ya ce idan ya bayyana dabarun zai tona wa hukumar sirrin lagon da za ta bi ta kama ejan masu sai wa ‘yan siyasa kuri’u.
Don haka ya ce dabarun a boye suke, ba za a bayyana su ga manema labarai ba.
Ya ce sai a ranar zabe za a rika bi ana yi wa dillalan cinikin kuri’u kamun-kazar-kuku.
A wasu zabuka da INEC ta gudanar cikin 2018, an sha fama da masu sayen kuri’u a hannun jama’a ana ba su abinci ko kuma ‘yan kudin da suka saukaka.
An kuma samun wuraren da aka rika saye da tsada Inda aka samu rahotannin sayen kuri’un sun hada da jihohin Anambra, Ondo, Oshun da Ekiti.
Discussion about this post